in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila rashin isasshen barci zai sa a yi kiba
2018-06-22 10:49:06 cri

Wani sakamakon nazari da masu nazari na kasar Birtaniya suka gudanar kan 'yan Birtaniya ya shaida cewa, rashin isasshen barci ya kan haddasa karuwar nauyin jikin dan Adam, har ma da matsalar kiba. Sa'an nan kuma, yanayin sarrafa sinadaran jikin mutane wadanda suke fama da rashin isasshen barci ba shi da kyau sam.

Masu nazari daga jami'ar Leeds ta kasar Birtaniya sun bayyana cikin rahotonsu cewa, sun tattara bayanan da suka shafi baligai 'yan Birtaniya 1615, dangane da tsawon lokacin barci, da yadda suke cin abinci, da samfur din jininsu da nauyin jikinsu. Sun kuma yi nazari mai zurfi kan alakar da ke tsakanin barci da lafiyar mutane. A karshe dai sun gano cewa, tsawon kugun mutanen, da matsakaicin lokacin barcinsu a ko wane dare ya kai awoyi 6, ya fi na wadanda matsakaicin lokacin barcinsu a ko wane dare ya kai awoyi 9 yawa ba, har da centimita 3. Galibi dai nauyin jikin wadanda ba su yi barci cikin dogon lokaci ya yi yawa.

Masu nazarin suna ganin cewa, sakamakon nazarinsu ya kara tabbatar da cewa, watakila rashin isasshen barci zai kara barazanar kamuwa da ciwon sukari, da sauran cututtukan da suka shafi yanayin sarrafa sinadaran jikin mutum. Sun kuma yi nuni da cewa, tun daga shekarar 1980 har zuwa yanzu, yawan masu fama da matsalar kiba a duk duniya ya ninka sau daya ko fiye da haka. Matsalar kiba ya kan haddasa cututtuka da dama; Alal misali, ciwon sukari nau'i na 2. Don haka kara sani kan dalilin da ya sa nauyin jikin dan Adam ke karuwa, yana da matukar muhimmanci wajen kiwon lafiyar al'umma yadda ya kamata.

Ban da haka kuma, sakamakon tantancewar ya nuna cewa, gajeren lokacin barci yana da nasaba da raguwar yawan sinadarin High-density Lipoprotein a cikin jikin dan Adam. Raguwar sinadarin ta kan haifar da wasu matsalolin lafiya. Yawan sinadarin High-density Lipoprotein a cikin jikin dan Adam yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Amma duk da haka, masu nazarin sun yi bayani da cewa, sun samu sakamakon nazarinsu ne, bayan da suka tantance bayanai masu yawa. Ba a iya samun sakamakon karshe ba. Akwai bambanci sosai a tsakanin mutane a fannin tsawon lokacin barci da suke bukata a ko wace rana. Amma yanzu yawancin masu ilmi suna ganin cewa, yawancin baligai ya fi dacewa su shafe awoyi 7 zuwa 9 a ko wace rana suna barci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China