in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan iyaye suna fama da matsalar kiba, sai kila yaransu kan samu jinkiri yayin da suke girma
2018-06-04 06:36:37 cri

Wani sakamakon nazari da kwalejin nazarin kiwon lafiya na kasar Amurka ta kaddamar ya shaida mana cewa, akwai yuwuwar yadda iyaye suke fama da matsalar kiba zai sanya yaransu samun jinkiri ta fuskar basira da kuma cudanya da mutane yayin da suke girma.

Sakamakon nazarin ya yi nuni da cewa, yaran da iyaye mata da nauyin jikinsu ya wuce misali suka haifa, ba sa amfani da kananan jijiyarsu yadda ya kamata, kamar yadda takwarorinsu suka yi amfani su kafin shekarunsu suka kai 3 a duniya. Sa'an nan kuma wasu yaran iyaye maza wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali su kan fuskanci matsalolin yin mu'amala da cudanya da mutane kafin shekarunsu suka kai 3 da haihuwa. Har ila yau, idan nauyin jikin dukkan iyayensu mata da maza ya wuce misali, yaransu kan fuskanci matsalar daidaita batutuwa, gwargwadon takwarorinsu wadanda iyaye masu matsakaicin nauyin jiki suka haifa.

A cikin wannan nazari, masu ilmin kimiyya daga kwalejin nazarin kiwon lafiya na kasar Amurka sun tantance bayanan da suka shafi mata dubu 5 mazauna jihar New York, wadanda suka taba haihuwa daga shekarar 2008 zuwa 2010. Yayin da yaransu suka kai watanni 4 da haihuwa, an gayyaci wadannan mata da mazajensu da kuma yaransu su shiga wata jarrabawa, inda daga baya suka amsa wasu tambayoyi, tare da gabatar da bayanan da suka shafi lafiyarsu da nauyin jikinsu kafin sun samu ciki da kuma bayan sun haihu da kuma lafiyar mijinsu da nauyin jikinsu. An kuma shigar da yaransu cikin wata jarrabawa ta daban, kafin shekarunsu suka kai 3 a duniya.

A cikin nazarce-nazarce da aka gudanar a baya, an mai da hankali kan illar da nauyin jikin iyaye mata kafin sun samu ciki da kuma bayan sun haihu ke yi kan yaransu. Sabon nazarin ya kuma nuna mana illar da nauyin jikin iyaye maza ya yi kan yaransu. Masu nazarin sun yi bayanin cewa, nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya kan dabbobi sun nuna cewa, yadda nauyin jikin iyaye mata yake wuce misali ya kan haifar da kunburi, lamarin da ke haifar da illa ga kwakwalwar 'yan tayi yayin da suke girma. Amma babu isassun bayanan da suka shafi yadda matsalar kiba da iyaye maza suke fuskanta take haddasa illa ga yadda yaransu suke girma. Wasu nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun nuna cewa, watakila matsalar kiba zai yi illa ga kwayoyin dabi'ar halitta da ke cikin maniyyi.

Masu nazarin sun tunatar da cewa, yanzu akwai kashi 1 cikin kashi 5 ne na masu juna biyu a kasar Amurka, wadanda nauyin jikinsu ya wuce misali, ko kuma suke sahun masu kiba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China