lafiya1816.m4a
|
Kwanan baya, wasu masu nazari na kasar Amurka sun gano cewa, idan masu juna biyu sun yi fama da matsalar rashin barci, da cutar "Sleep Apnea" da sauran matsalolin barci, hakan na sanya su kara fuskantar barazanar haihuwar jariransu da wuri. "Cutar Sleep Apnea", wanda ake kuma kira da cutar barci ta Apnoea, yanayi ne dake haifar da daukewar numfashi, ko karancin numfashi yayin bacci. Kaza lika dakatawar numfashi na faruwa ne na 'yan dakiku, sannan suna faruwa sau da yawa a dare daya.
A yawancin lokuta, tsawon lokacin zama mai juna biyu ya kan kai makonni 40 baki daya. Ma'anar haihuwar jarirai da wuri, ita ce haihuwar jarirai kafin tsawon lokacin zama mai juna biyu ya cika makonni 37.
Masu nazari daga reshen jami'ar California ta kasar Amurka da ke birnin San Francisco, sun kaddamar da rahoton nazarinsu a kwanan baya, cikin mujallar "ilmin kula da mata da mata masu juna biyu" ta kasar Amurka, inda suka nuna cewa, bayan da suka tantance bayanan lafiyar mata kusan miliyan 3, da kuma haihuwarsu daga shekarar 2007 zuwa ta 2012 a jihar ta California. Sun dai gano cewa, idan masu ciki suna fama da matsalar rashin barci, suna fuskantar barazanar haihuwar jarirai da wuri da karuwar kashi 30 cikin dari. Idan masu ciki suna fama da cutar Sleep Apnea, barazanar haihuwar jarirai da wuri da suke fuskanta za ta karu da kashi 40 cikin dari.
Ban da haka kuma, in an kwatanta su da masu juna biyu wadanda ba su da matsalar barci, wadanda suke fama da matsalar rashin barci, ko kuma cutar Sleep Apnea, su kan fuskanci karuwar haifar jairai kafin tsawon lokacin zama mai juna biyu ya cika makonni 34, har sau biyu.
Masu nazarin suna ganin cewa, ko da yake nazarinsu ta shaida mana alakar da ke tsakanin matsalar barci da kuma haihuwar jarirai wuri, amma ba a san dalilin da ya sa hakan ba tukuna. Sun kiyasta cewa, watakila rashin barci zai haifar da kunburi da sauran matsalolin lafiya, a karshe dai masu juna biyu suna iya haihuwa da wuri.
Masu nazarin sun yi bayani da cewa, ya zuwa yanzu haihuwar jarirai da wuri, tana addabar likitocin kula da haihuwa a duk duniya. Nazarinsu ya nuna cewa, mai yiwuwa ne fitar da dabarun tabbatar wa masu juna biyu isasshen barci, zai taimaka wajen daidaita matsalar haihuwar jarirai da wuri. (Tasallah Yuan)