in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bada shawarar rabawa uwa da jaririnta gadon kwanciya domin kaucewa mutuwa ba zato ba tsammani
2018-04-16 07:51:29 cri

Kwanan baya, hukumar ilmin jinyar kananan yara ta kasar Amurka ta kaddamar da sabon littafin ba da shawara kan kare jarirai daga mutuwa ba zato ba tsammani, inda ta yi bayani da cewa, da zummar rage barazanar mutuwar jarirai ba zato ba tsammani, kamata ya yi jarirai sabbin haihuwa su yi barci tare da iyayensu a daki guda amma a gado daban daban kafin shekarunsu su kai 1 a duniya, musamman ma wadanda ba su wuce watanni 6 a duniya ba.

Wannan hukuma mafi girma ta Amurka a fannin ilmin jinyar kananan yara, ta yi karin bayani da cewa, abubuwan shaida sun nuna cewa, matakin da muka ambata a baya zai iya rage barazanar da jarirai suke fuskanta ta fuskar mutuwa ba zato ba tsammani da kashi 50 cikin dari.

Hukumar ta kuma ba da shawarar cewa, kamata ya yi iyaye su bar jariransu su yi barci a rub da baya a kan gado mai tauri. Kada su shimfida katifa mai laushi, da kuma marufin gado mai sako-sako a kan gadon, sa'an nan kada su ajiye bargon ulu a kai, da matashin kai da abubuwan wasa wadanda aka yi da atamfa mai dogon gashi a kan gadon.

Babban marubucin wannan littafin ba da shawara kan kare jarirai daga mutuwa ba zato ba tsammani ya bayyana cewa, ko kusa kada iyaye su bar 'ya'yansu su yi barci a kan doguwar kujerar zama a falo, ko kujera da ke da katifa mai laushi, ko dai su kadai ko su da wasu. Kowa ya san cewa, dukkan wadannan kayayyakin gida da ke da katifa mai laushi, suna da matukar hadari.

Har ila yau, hukumar ta yi nuni da cewa, shayar da jarirai da nonon iyayensu mata, yana taimakawa wajen rage barazanar mutuwar jariran ba zato ba tsammani, amma ya zama tilas iyaye mata su lura da cewa, kada su yi barci yayin da suke shayar da jariransu nononsu. Idan iyaye mata sun ji za su yi barci yayin da suke shayar da jariransu nononsu, to, ya fi kyau su shayar da jariransu nonon a kan gado, a maimakon kujerar zaman falo, ko kujerar da ke da katifa mai laushi, kana kuma kada a ajiye matashin kai da bargon ulu a kan gadon.

Ma'anar mutuwar jarirai ba zato ba tsammani ita ce jarirai wadanda ga alama suke cikin koshin lafiya su mutu ba zato ba tsammani, musamman ma a lokacin da suke barci. Mutuwar jarirai ba zato ba tsammani, wani muhimmin sanadi ne da ke haifar da mutuwar jariran da shekarunsu ba su kai 1 a duniya ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China