in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Na saurari shirin Gani Ya kori ji
2018-03-16 16:48:20 cri
A ranar laraba 14 ga watan Maris shekara ta 2018 da yammaci, na samu zarafin sauraron shirin ku na Gani ya kori ji wanda malama IbrahimYaya da Ahmad Inuwa Pagam suka jagoranta. Malaman sun yi tsokaci ne a dangane da muhimman taruka biyu da aka saba yi a duk shekara a kasar Sin. Babu shakka, tsokacin da malamai Ibrahim Yaya da Ahmad Inuwa Pagam suka yi mana a cikin ya kara mana ilmi da fahimta da kuma wayin kai game da manyan tarukan 2 wato Npc da kuma cppcc wanda ke da fa'ida sosai ga rayuwar sinawa da gwamnatin kasar Sin da ma kasashen ketare, masamman ga kasashenmu na Afirka masu tasowa.

Ni abunda ya fi bani sha'awa game da taruka 2 na shekarar bana(2018) shi ne yadda aka kara ba wa dukkan kabilu kanana da manya damar samun wakilci da kuma karin kuzari na su gabatar da nasu shawara ko ra'ayi adangane yanayin rayuwa da kuma yadda za a kara bada kuzari ta yadda za a kara sa kaimi game yadda za a kara yalwata habakar bunkasuwar sabuwar kasar Sin ta zamani mai al'umma mai godaro da kai. Kana sha'awarar da aka gabatar ga mahalarta wannan muhimman taruka 2 a dangane da aiwatar da gyaran fuska a kundin tsarin mulkin kasar Sin ta yi ma'ana kuma ta bada dama ga karin zarafin samun walwala da jin dadin rayuwar sinawa kana hakan ka iya kara bude wani saban babi na gina sabuwar kasar Sin ta zamani.

Kana yadda shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya yi wata ganawa ta masamman da wakilan kananan kabilun kasar China, domun wannan ganawa da shugaan kasar China mr. Xi Jinping ya yi da wakilan kananan kabilun kasar Sin, wata alama ce dake alamunta yadda gwamnatin kasar Sin suka ba wa kowace kabilar damar su ma a dama da su, a gaskiya hakan ya burgeni sosai yadda ya kamata. Da fatan sauran kasashen duniya, masamman ma kasashenmu na Afirka za su hanzarta daukan darasi kana kuma su yi koyi da gwamnatin kasar Sin adangane da abunda aka tattauna a zauren yin taruka 2 dake birnin Beijing na kasar Sin, ameen.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China