in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Huldar Diplomasiyya a tsakanin Sin da Nigeria
2018-01-27 13:09:47 cri
Yayin da kasashen taraiyar Nigeria da aminiyarta kasar Sin ke shirye-shiryen bukukuwan murnar cika shekaru 47 da kafuwar huldar diplomasiyya a tsakanin kasashen 2, muna ganin cewa, kasashen taraiyar Nigeria da aminiyarta jamhuriyar jama'ar Sin da al'ummominsu sun samu ci gaba mai yawan gaske ta fannin samun moriya da kuma samun bunkasuwar kasuwanci da habakar diplomasiyya da musayar ilmi da al'adu da kuma bunkasa harkokin mu'amula da juna da kasuwanci bisa manyan tsare-tsare da harkokin wanzar da aiyukan raya kasa masu nagarta da karko da suka hada da shinfida layukan dogo, masamman ma layukan dogo da kasar Sin suka shinfida daga birnin taraiyar Nigeria Abuja zuwa birnin Kaduna. Babu shakka, kasar Sin ta aiwatar da muhimman aiyukan raya kasa tare da samar da abubuwan more rayuwa mai masu kyau da nagarta a kasarmu taraiyar Nigeria. Muna fata kasashen 2 za su kara yaukaka huldar jakadanci dake akwai a tsakanin kasashen 2 a wasu karin shekaru masu zuwa, ameen.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China