lafiya1802.m4a
|
Jami'ar Ehime ta kasar Japan ta kaddamar da wani rahoto a kwanakin baya, wanda manazarta a jami'ar da na jami'ar Tokyo suka hada kai wajen aiwatar da wani bincike da ya shafi masu juna biyu dubu 1 da dari 7 da 45. Masu nazarin ba su yi la'akari da wasu abubuwan da za su yi tasiri ko illa kan nazarinsu ba, kamar shan taba, kudin shiga da shekarunsu a duniya, inda suka tantance halin da masu juna biyun suke ciki game da yanayin tunani da kuma yawan wake da su kan ci yau da kullum.
Masu nazarin sun raba wadannan masu juna biyu zuwa rukunoni guda 4 bisa yawan waken da su kan ci a zaman yau da kullum. Sun sa muhimmanci wajen yin nazari kan alakar da ke tsakanin yawan wake da a kan ci da kuma shiga cikin bakin ciki a lokacin samun juna biyu.
Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, a cikin dukkan wadannan masu juna biyu da suka shiga nazarin, wasu da yawansu ya kai kashi 19.3 cikin dari ne suka yi fama da bakin ciki yayin da suke samun ciki. Kuma idan suna kara cin wake a lokacin da suke da ciki, yawansu na raguwa. Idan an kwatanta masu juna biyu da suka fi cin wake, matsakaicin yawan wake da su kan ci a ko wace rana ya kai wa giram 93, yayin da wadanda su kan ci wake kadan, ke cin giram 21 a ko wace rana, sai yawan wadanda suka kamu da bakin ciki ya ragu da kashi 37 cikin dari.
Masu nazarin suna ganin cewa, yawan sinadarin Female Hormone ya na sauyawa sosai kafin masu juna biyun su haihu, da kuma bayan haihuwa, lamarin da ya kan sa su kamu da bakin ciki. Amfanin sinadarin Isoflavone da ke akwai cikin wake ya yi kama da amfanin sinadarin Female Hormon, abun da ka iya taka rawa wajen kare mata daga kamuwa da bakin ciki. (Tasallah Yuan)