in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shekara ta 2017 ta zo karshe- daga kungiyar masu sauraron rediyon kasar Sin Cri ta jihar sokoto
2017-12-26 14:10:06 cri
kungiyar masu sauraron rediyon kasar Sin Cri,

Ta jihar sokoto P. O. Box 4039 sokoto,

Sokoto state,

Nigeria.

Ina mai amfani da wannan dama in dan yin jinjina da yabo ga shuwagabannin jammaiyar kwaminis na kasar Sin baki daya tare da jinjina ga kafar watsa lalarrun kasar Sin wato Cri sabo da gagarumar gudunmuwar da take bayarwa domin samar da ci gaban kasar Sin tare da yada manufofin kasar Sin zuwa ga kasashen duniya baki daya.

Bama kawai kasar Sin a shekara mai karewa ta samar da gagarumar gudunmuwa ga kasar Sin da kasashenmu na afrika da Asiya da Turai da Amurka baki daya, a hannu daya dauwa uba da samar daga garumar gudunmuwa game zauren majalisar dinkin duniya baki daya.

A shekara ta 2017 abubuwa da dama sun wakana tsakanin Sin da kasashen duniya baki daya kamar haka.

1. A farkon shekara shugaba Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai ma'ana tare da sosarai ga duniya baki daya wajen sanar da duniya irin ci gaban da za ta samar ta ko wanen fannin na rayuwa musamman ci gaban tattalin arzikin kasashen du iya baki daya.

2. A shekarar mai karewa ta 2017 kasar Sin ta gudanar da babban taron hadin guiwa na duniya mai taken hanya daya ziri daya mai samar da walwala ta fannoni daban daban ga kasashenmu na duniya da suka hada ko wace nahiya ta duniya, tare da samar da turban tattalin arzikin duniya baki daya.

3. A shekara mai karewa kasar Sin ta samar da gagarumin tallafi ga kasashenmu na Afrika wanda ya shafi ko wane fanni na rayuwa domin mu samu ci gaba da dogaro gakammu tare da aiwatar da yarjejeniyan da kasashen BRICs suka cinma a shekarrun da suka gabata.

4. Ba shekka kasar Sin da shugaba Xi Jinping sun ba da gagarumar gudunmuwa ta fannin ci gaban masana'antu da yawon shakatawa tsakanin kasar Sin da nahiyarmu ta Afrika dama duniya baki daya, har wa yau Sin tana ba da gagarumar kulawa ga dukkanin kasashen makwattanta Kamar su Vietnam, Mongoliya, India, Rasha da dai makamantansu tare da samar da dukkanin abin da ya dace a garesu.

5. Idan muka duba ta fannin watsa labarru sashen Hausa na Cri ya sami jinjina a garemu sabo da muna samin cikakun bayanai a kan irin wainarda ake toyawa a kasar Sin da sauran kasashen duniya baki daya a wannan shekara mai karewa ta 2017, muna samun dukkanin sakonn inda kuka aiko muna wadanda keda muhimmamci a garemu Kamar mujallarlum zumunta na Hausa da sauran kautuntuka da kuke aiko muna a ko da yaushe muna godiya.

6. Daga karshe muna jinjina ga dukkanin shuwagabannin kasasr Sin da gidan rediyo Cri musammam sashen Hausa da dukkanin maaikatakun baki daya fatarmu a shigo sabuwar shekara ta 2018 lafiya ameen , daga mai sauraronku a ko da yaushe.

Bello Abubakar Malam Gero ,

Kmscri sokoto.

Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China