in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aure yana taimakawa wajen tsawaita tsawon ran masu fama da ciwon sankara
2017-12-18 06:18:01 cri

Masu nazari sun gano wani amfani na daban da aure yake da shi! An kaddamar da sakamakon wani nazari a mujallar Ciwon sankara ta kasar Amurka, wanda ke nuna cewa, masu fama da cutar daji wadanda suke da aure, sun fi tsawon rai, idan aka kwatanta da takwarorinsu wadanda ba su da aure.

Masu nazari daga cibiyar nazari da rigakafin cutar daji ta jihar California dake kasar Amurka, da rashen San Diego na jami'ar California dake kasar, sun tantance baligai kusan dubu 800 mazauna jihar California, wadanda aka gano sun kamu da ciwon sankara tsakanin shekarar 2000 zuwa ta 2009, sun kuma sake bibiyar su ya zuwa shekarar 2012.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, yawan mutuwar masu fama da ciwon sankara ga wadanda ba su yi aure ba, ya fi na takwarorin wadanda suke da aure yawa.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, muhallin da ake ciki ta fuskar tattalin arziki, ba wani dalili ne da ya haddasa irin wannan adadin mutuwa ba.

Nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya, sun riga sun tabbatar da wani nau'in kariyar da aure yake bayar wa dan Adam. Amma nazarin da masu nazarin Amurka suka gudanar, ya zama na farko, da aka gudanar cikin dimbin mutane. Kana kuma an kimanta tasiri ko illa da wasu batutuwa suke haifarwa kan sakamakon nazarin; Alal misali, muhallin da masu fama da ciwon suke ciki ta fuskar tattalin arziki.

Har ila yau, masu nazarin sun gano cewa, irin wannan kariya da aure yake bayarwa, ta sha bamban a tsakanin Amurkawa 'yan asalin kasashe daban daban. Fararen fata 'yan asalin wuraren da ba kasar Spaniya ba, sun fi samun kariya mai kyau, yayin da 'yan asalin kasar Spaniya, da 'yan asalin kasashen Asiya, da 'yan asalin tsibiran da ke tekun Pasific, ba su da kariyar yadda ya kamata.

A ganin masu nazarin, watakila dalilin da ya sa haka shi ne domin baya ga ma'auratansu, 'yan asalin kasar Spaniya, da 'yan asalin kasashen Asiya, da 'yan asalin tsibiran da ke tekun Pasific na kulla dankon hulda a tsakaninsu da iyalansu da kuma abokansu. Amma Fararen fata 'yan asalin ba kasar Spaniya ba su da irin wannan hulda ta zaman al'umma a kasar su.

Masu nazarin sun nuna cewa, samun goyon baya daga zaman al'ummar kasa, musamman ma daga maaurata, yana taimakawa sosai wajen tsawaita tsawon ran masu fama da ciwon sankara. Sun ba da shawarar cewa, yayin da likitoci suka ba da kulawa ga masu fama da cutar daji wadanda ba su yi aure ba, ya kamata su tambaye su ko za su iya samun isasshen goyon baya daga iyalai, ko abokai ta fuskar jiki da tunani. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China