in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hauhawar nauyin jiki cikin wani wa'adi tana iya kara barazanar kamuwa da cutar daji
2017-12-10 11:28:34 cri

Kwanan baya, jami'ar Manchester ta kasar Ingila ta kaddamar da sakamakon wani nazari, inda ta yi nuni da cewa, idan wani ko wata ta samu hauhawar nauyin jiki sosai cikin wani wa'adi, hakan yana iya kara musu barazanar kamuwa da cutar daji, musamman ma maza da suka fi fuskantar irin wannan barazana.

Masu nazari daga jami'ar Manchester da cibiyar nazari kan yanar gizo game da lafiyar mutane, sun dauki dogon lokaci suna sake bibiyar bayanan lafiyar Amurkawa kusan dubu 300, ciki har da maza 177,500 da mata 111,500. Masu nazarin sun rubuta sauye-sauyen mizanin BMI na awon nauyin mutum, da yawan mutanen da suka kamu da ciwon sankara sakamakon matsalar kiba.

Mizanin BMI, mizani ne na awon nauyin mutum a kilogiram a raba da tsayin mutum a mita sikwaya. A kan yi amfani da mizanin a duk fadin duniya. Yawancin mutane suna ganin cewa, idan mizanin BMI ya wuce 25, nauyin jikin mutum ya wuce misali. Idan mizanin ya wuce 30, to mutumin yana kan sahun masu kiba.

Nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya sun shaida mana cewa, akwai alaka a tsakanin yadda nauyin jikin mutum da ya wuce misali, ko mutumin yana kan sahun masu kiba, da kuma barazanar kamuwa da ciwon sankara a uwar hanji, da saifa, da cikin mama, da mahaifa da dai makamantansu. A cikin sake bibiyar da masu nazarin suka yi a wannan karo, kimanin mata 9400, da maza 5500 sun kamu da irin wannan ciwon sankara bayan da shekarunsu sun kai 65 da haihuwa.

Masu nazarin sun gano cewa, idan mizanin BMI na awon nauyin maza ya karu daga 22 zuwa 27, barazanar kamuwa da cutar daji da suke fuskanta za ta karu da kashi 50 cikin dari. Sa'an nan kuma, idan mizanin BMI na awon nauyin mata ya karu daga 23 zuwa 32, to irin wannan barazanar da suke fuskanta za ta karu da kashi 17 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu yana taimakawa mutane su kara fahimtar su wane ne suke matukar bukatar daukar matakai domin rage kiba, domin kokarin kaucewa gamuwa da matsalolin lafiya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China