in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan maganin Aspirin a ko wace rana yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara a kwan mace
2017-12-01 08:12:27 cri

Wani sabon nazari da cibiyar nazarin ciwon sankara ta kasar Amurka ta gudanar ya nuna mana cewa, shan maganin Aspirin a ko wace rana, yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara a kwan mace, har da kashi 20 cikin dari. Amma masu nazarin sun jaddada cewa, ana bukatar ci gaba da nazarin na su domin ba da shawara mafi dacewa.

Ciwon sankara a kwan mace yana daya daga cikin cututtukan da suke kawo wa lafiyar mata barazana. A ko wace shekara, a kasar Amurka kawai mata fiye da 20,000 dake kamuwa da ciwon sankara a kwansu, yayin da wasu 14,000 suke rasa rayukansu sakamakon ciwon. Idan an gano mace ta kamu da ciwon da wuri, ana iya yi mata jinya yadda ya kamata, kuma za ta iya warkewa. Amma alamun kamuwa da ciwon sankara a kwan mace sun yi kama da na sauran cututtukan sankara, don haka kullum ana iya makarar gano mace ta kamu da ciwon sankara a kwanta.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, idan mace tana fama da matsanancin ciwon sankara, tana jiran lokaci ne kawai, domin jinyar da za a iya ba ta ba ta da yawa, kuma ba za ta iya samun sauki kamar yadda ake fata ba. Don haka matakan yin rigakafi suna da matukar muhimmanci, wajen daidaita ciwon sankara a kwan mace.

Nazarce-nazarcen da aka yi a baya sun shaida mana cewa, shan maganin Aspirin a ko wace rana, yana iya rage barazanar kamuwa da ciwon sankara a uwar hanji, fata da dai sauransu. Don haka, masu nazarin na kasar Amurka sun gudanar da nazari mafi girma kan alakar da ke tsakanin shan maganin Aspirin da barazanar kamuwa da ciwon sankara a kwan mace.

Masu nazarin sun tantance bayanan da suka shafi masu fama da ciwon sankara a kwan mace dubu 8, da kuma mata masu koshin lafiya kusan 12000, wadanda wasu kashi 18 cikin dari suna shan maganin Aspirin. Masu nazarin sun gano cewa, in an kwatanta matan da ba shan maganin Aspirin sau daya a ko wane mako, barazanar kamuwa da ciwon sankara a kwan mace da wadanda suke shan maganin a ko wace rana suke fuskanta na raguwa da kashi 20 cikin dari.

Amma duk da haka masu nazarin sun jaddada cewa, suna bukatar zurfafa nazarinsu, domin kara sanin daidaito a tsakanin barazanar da maganin na Aspirin za ta iya yi, da kuma amfaninsa.

Har ila yau masu nazarin sun yi kashedi da cewa, tilas ne a samu iznin likita kafin a sha maganin Aspirin a ko wace rana. Saboda maganin yana haifar da fidda jini a kayayyakin jiki masu narka abinci, da kuma shan inna sakamakon fid da jini a kwakwalwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China