in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan masu juna biyu suna shan abubuwan dake da sinadarai masu zaki nauyin jariransu zai wuce misali
2017-11-19 10:32:41 cri

A kwanakin baya ne masu nazari daga kasar Canada suka kaddamar da wani rahoto dake cewa, idan masu juna biyu su ka yawaita sha abu mai cike da sinadarai masu zaki da aka sarrafa kullum, to watakila yin hakan na iya sa nauyin jariransu ya wuce misali cikin sauki.

Nazarin da aka gudanar kan iyaye mata fiye da dubu 3 da kuma jariransu ya shaida cewa, wasu da yawansu ya kai kusan kashi 30 cikin dari na wadannan mata sun taba shan wani abu mai cike da sinadarai masu zaki da aka sarrafa, kamar abin sha dake rage kiba, ruwan lemu, shayi da kofin da aka sa sinadarai masu zaki a ciki, a lokacin da suke da juna biyu, a cikinsu kuma, wasu kashi 5.1 cikin dari su kan sha irin wadannan abubuwa masu cike da sinadarai masu zaki da aka sarrafa a ko wace rana.

Masu nazarin sun bayyana cewa, yayin da suke gudanar da nazarinsu, ba su yi la'akari da matsalar kiba da iyaye mata suke fuskanta da kuma yanayin ci da shansu ba. Sun gano cewa, idan masu juna biyu su ka yawaita shan wasu abubuwa masu cike da sinadarai masu zaki da aka sarrafa a ko wace rana, to, yayin da shekarun kananan yaransu suka kai 1 a duniya, nauyin yaran nasu ya kan wuce misali, kuma irin wannan barazanar da suke fuskanta ta ninka sau biyu idan aka kwatanta da na sauran takwarorinsu.

Ana ganin cewa, sukari yana haddasa kiba saboda yana cike da abubuwa masu jina jiki. Don haka masana'antu su kan yi amfani da sinadarai masu zaki da aka sarrafa wadanda ba su da abubuwa masu gina jiki a cikin abun sha a madadin sukari. Duk da haka wasu nazarce-nazarce sun shaida mana cewa, yin amfani da sinadarai masu zaki da aka sarrafa cikin dogon lokaci zai kara barazanar yin kiba da kamuwa da wasu cututtukan da suka shafi sinadaran da jiki ke bukata.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, nazarinsu ya tabbatar da cewa, yadda masu juna biyu su kan sha abubuwa masu cike da sinadarai masu zaki da aka sarrafa kullum, zai yi tasiri ga nauyin jariransu. Yanzu matsalar kiba ta zama ruwan dare a tsakanin kananan yara, kana kuma ana amfani da sinadarai masu zaki da aka sarrafa a abubuwa daban daban, don haka ana bukatar kara tabbatar da sakamakon nazarinsu, tare da kara sanin dalilan da ke haddasa haka, ta yadda za a iya bai wa masu juna biyu kyakkyawar shawara dangane da yadda suke ci da shan abubuwa. Kafin a samu isassun bayanai game da wannan batu,kamata ya yi masu juna biyu su rika shan ruwa mai tsafta domin biyan bukatunsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China