in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Koyawa jarirai kide-kide yana taimaka musu wajen koyon yin magana
2017-11-13 06:52:22 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a jami'ar Washington ta kasar Amurka ya yi nuni da cewa, koyawa jarirai kide-kide, watakila yana taimaka musu wajen koyon yin magana.

Masu nazari daga cibiyar nazarin kwakwalwa da karatu ta jami'ar Washington ta Amurka sun bayyana cewa, a karo na farko nazarinsu ya tabbatar da cewa, a cikin muhimmin lokacin da jarirai suke koyon yin magana, ba kawai yadda ake magana a kewayensu ya kan yi tasiri kan kwarewarsu na koyon yin magana ba, haka ma kide-kide suke yi.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, jarirai suna koyon bayanai iri daban daban daga muhalin da suka samu kansu. Kide-kide, wani nau'in bayani ne mai muhimmanci, wanda watakila suke yin tasiri kan kwakwalwarsu da kuma taimaka musu yayin da suke girma.

Masu nazarin sun tsara wasu bayanai domin tabbatar da cewa, ko koyon kide-kide zai iya taimaka wa jarirai wajen koyon yin magana. Sun kuma yi nazari kan yadda jariran suka fahimci yanayin ko salon kide-kide. Yanayin kide-kide yana taimaka wa mu 'yan Adam wajen dakatawa yayin da muke magana, fahimtar ma'anar magana da bambanci mabambantan karin sauti, kana kuma yana da muhimmanci wajen amfani da kide-kide yayin koyon yin magana.

A cikin wata guda da aka gudanar da nazarin, an raba jarirai 39 da shekarunsu suka kai watanni 9 a duniya zuwa rukunoni guda 2 da ka, a cikinsu kuma wasu 20 aka yi musu kide-kide, kuma an koyar da mahaifansu yadda za su taimakawa jariran nasu da tafi, suna kada ganga suna kuma yi musu kide-kiden. Sauran jariran 19 kuma, an bar su yi wasa da abubuwan wasa daban-daban wadanda suke sha'awa, amma ba a yi musu kide-kide ba.

Masu nazarin sun yi abun da muka ambata a baya cikin mintoci 15 kuma har sau 15 a cikin wata guda. Daga baya, masu nazarin sun yi wa dukkan jariran kide-kide, tare da yin amfani da wata na'urar daukar hotuna ta musamman don binciken kwakwalwar dukkan jariran, domin ganin yadda jariran suke mayar da martani kan amon da suke saurara a kwakwalwarsu.

Kamar yadda masu nazarin suke hasashe, koyawa jariran kide-kide yana taimaka musu wajen kyautata kwarewarsu ta fahimtar salon kide-kide.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, kwarewar fahimtar salon kide-kide, wata muhimmiyar kwarewa ce ga dan Adam. Watakila kyautata kwarewar kananan yara ta hanyar fahimtar salon kide-kide za ta yi tasiri kan yadda suka yi karatu cikin dogon lokaci.

Duk da haka sun yi nuni da cewa, a cikin nazarinsu, sun koya wa jariran yadda za su rika tafi da hannusu, ko kada ganga tare da kide-kide. Ba su san wani irin tasiri hakan zai yiwa jarirai yayin da aka yi musu kide-kide kawai ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China