in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jarirai kan yi kiba cikin sauri idan sun fara yin amfani da gorar shayar da jarirai madara kafin lokacin da ya dace
2017-11-06 06:53:01 cri

Kwanan baya masu nazari daga kasar Amurka sun kaddamar da rahoton nazarinsu a shafin internet na mujallar "sashen kula da yara kanana", inda suka nuna cewa, nauyin jarirai wadanda suka fara yin amfani da babbar gorar shayar da jarirai madara jim kadan bayan haihuwarsu, sun fi na wadanda su kan yi amfani da karamar gorar shayar da jarirai saurin karuwa. Har ma bayan da suka girma, su kan fuskanci barazanar yin kiba.

Masu nazari daga sashen Chapel Hill na jami'ar North Carolina ta kasar Amurka sun gudanar da bincike kan jarirai 386 wadanda suke shan garin madara, a karshe sun tattara bayanan da suka shafi jarirai 298, a cikinsu wasu kashi 44 cikin dari suna amfani da babbar gorar shayar da jarirai madara da ta wuce girman Milliliter 180 bayan haihuwarsu. Masu nazarin sun tantance karuwar nauyin wadannan jarirai duka a lokacin da shekarunsu suka kai watanni 2 da kuma watanni 6 da haihuwa.

Sakamakon nazarin ya shaida cewa, matsakaicin nauyin dukkan wadannan jarirai ya kai kilo 3.2 daidai bayan da aka haife su. Bayan watanni 2, matsakaicin nauyin su ya kai kilo 5.3, yayin da matsakaicin nauyin su ya kai kilo 8 a lokacin da suka kai watanni 6 da haihuwa. Matsakaicin nauyin jariran da suke amfani da babbar gorar shayar da jarirai madara ya kai kilo 5.4 a lokacin da suka kai watanni 2 a duniya. Matsakaicin nauyin su ya kai kilo 8.2 a lokacin da suka kai watanni 6 a duniya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, akwai bambanci a tsakanin ko wane jariri. Amma duk da haka, gorar shayar da jariran wadda girmanta ya kai Milliliter 120 ta fi dacewa da jariran da suka kai watanni 2 a duniya. Gwargwadon jarirai wadanda aka shayar da su nonon uwa zalla, jariran da suke shan garin madara a gora kullum su kan sha garin madara fiye da kima, musamman ma a kan tilasta musu shanye garin madara da ya saura cikin gorar. Sannu a hankali, nauyin jariran ya kan karuwa fiye da kima, har ma lamarin ya kara kawo musu barazanar yin kiba sakamakon cin abinci da yawa bayan da suka yi girma. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China