in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Murmushi yana iya kyautata yanayin jikin dan Adam
2017-10-17 10:37:48 cri
Sinawa kan ce, murmushi na kyautata yanayin jikin dan Adam. Kwanan baya, masu nazari daga kasar Japan sun tabbatar da cewa, tsoffafin da su kan yi murmushi sun fi gamsuwa da yanayin jikinsu. A baya, sun gano cewa, wadanda ba su gamsu da yanayin jikinsu ba sun fi fuskantar matsalar kwanciya a gado sakamakon kamuwa da ciwo da kuma karuwar mutuwa. Saboda haka, masu nazarin suna ganin cewa, mai yiwuwa ne tsoffafin da su kan yi murmushi sun fi samun kyaun yanayin jiki. Tawagar masu nazari na jami'ar Tokyo ta hada kai da takwarorinta na jami'ar Osaka, wajen gudanar da wani bincike kan tsoffafi kimanin dubu 20 a duk fadin kasar ta Japan, wadanda shekarunsu suka zarce 65 a duniya, domin tabbatar da alakar da ke tsakanin yawan murmushi da su kan yi da kuma yanayin jikin tsoffafin. Nazarinsu ya shaida mana cewa, a cikin zaman rayuwar yau da kullum, kusan mazan da yawansu ya kai kashi 38 cikin dari da kuma matan da yawansu ya kai kashi 49 cikin dari ne su kan yi dariya a ko wace rana. Sa'an nan kuma, mazan da yawansu ya kai kashi 10 cikin dari da kuma matan da yawansu ya kai kashi 5 cikin dari ne ba su taba yin dariya ba. Bayan da masu nazarin suka tantance alakar da ke tsakanin yawan murmushi da suka yi da kuma yadda suka siffanta yanayin jikinsu, sun gano cewa, a cikin tsoffafin da ba su taba yin murmushi ba, yawan wadanda ba su gamsu da yanayin jikinsu ba ya ninka sau 1.54 gwargwadon tsoffafin da su kan yi murmushi a ko wace rana, yayin da yawan wadanda a ganinsu, yanayin jikinsu ba shi da kyau sam ya ninka sau 1.78 gwargwadon tsofaffin da su kan yi murmushi a ko wace rana. Nazarin da wadannan masu nazarin na Japan suka gudanar a baya ya shaida cewa, idan wasu sun kara gamsuwa da kyaun yanayin jikinsu, za su kara nisantar da kansu daga matsalar kwanciya a gado sakamakon kamuwa da ciwo da kuma mutuwa. Masu nazarin na Japan sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya nuna mana cewa, mai yiwuwa ne idan tsoffafi suka yawaita yin murmushi, za su kara samun kyaun yanayin jiki. Ko da yake ana bukatar ci gaba da nazari kan dalilin da ya sa hakan, amma duk da haka, ya fi kyau tsoffafi su kara yin dariya a zaman na yau da kullum domin kara samun kyaun yanayin jikinsu. (Tasallah Yuan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China