in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dole ne a mai da hankali kan ba da agajin gaggawa a hankalin dan Adam
2017-10-08 11:46:43 cri

Ranar 10 ga watan Oktoba, rana ce ta kiwon lafiyar kwakwalwar dan Adam ta duniya. A Kwanakin baya, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta jaddada muhimmancin ba da agajin gaggawa ga kwakwalwar dan Adam. Ta kuma ba da shawarar cewa, ya kamata a kara sanin muhimman ka'idojin ba da agajin gaggawa ga kwakwalwar dan Adam, tare da nuna goyon baya da tallafawa wadanda suka ji rauni a kwakwalwarsu. Abu mafi muhimmanci shi ne a kara sanin abubuwan da aka ambata.

Cikin takardar dake kunshe da bayanai kan ba da agajin gaggawa ga kwakwalwar dan Adam da hukumar WHO ta kaddamar a shafinta na Internet, ta bayyana cewa, tilas ne a ba da agajin gaggawa ga kwakwalwar wadanda munanan bala'u daga indallahi, hare-haren ta'addanci, barkewar cututtuka, hadarurruka suka rutsa da su, ko kuma wadanda aka yi wa fashi. Ba kwararru kadai ne suka iya ba da agajin gaggawa ba. Idan wadanda abin ya shafa suka samu agajin gaggawa a cikin lokaci, zai taimaka sosai ga lafiyar kwakwalwarsu cikin dogon lokaci.

WHO ta sa muhimmanci sosai kan tunatar da mutane da cewa, idan an kula da wadanda suka fada cikin bakin ciki, to kada a tilasta musu yin bayani kan abun da ya faru da su, sannan kada a bayyana ra'ayi kan abun da ya faru da su, a magance gaya musu cewa, "bai kamata ba kana ganin hakan", ko kuma "dole ne ka ji ka taki sa'a saboda ka rayu". Sa'an nan kuma, kada a yi alkawarin da ba za a iya cika ba. Kada a gaya wa wanda abin ya shafa abubuwan da suka faru a kan wasu. Kada a ambato matsalar da ake fuskanta.

Har ila yau, WHO ta jaddada cewa, a maimakon taimakawa wanda abin ya shafa su tantance abun da ya faru a kansa, ya kamata masu ba da agajin gaggawa su lura da biyan manyan bukatunsu, kamar samar musu abinci da abin sha. Kuma abu mafi muhimmanci shi ne su saurari maganarsu a tsanake, su ba su bayanan da suke bukata, su taimaka musu kwantar da hankalinsu, a kokarin taimaka wa wadanda abin ya shafa su ji suna iya samun goyon baya daga iyalinsa da sauran jama'a, suna iya sarrafa zaman rayuwarsu da kansu. Bayan haka kuma, kamata ya yi a gaya wa wanda abin ya shafa cewa, suna iya samun taimako a yanzu, amma nan gaba za su iya samun taimako da kuma goyon baya a ko da yaushe.

Kididdigar hukumar ta WHO ta shaida mana cewa, a ko wace shekara, mutane kimanin miliyan daya suna kashe kansu sakamakon matsalar kwakwalwa a duk duniya. Kisan kai da kai, ya zama babban dalili na uku da ke haifar da mutuwar matasa. A cikin kasashe masu tasowa, nakasassun da yawansu ya kai kashi 19.1 cikin dari, wadanda suka nakasa bayan sun girma sun nakasa ne saboda bakin ciki da shan giya fiye da kima sakamakon matsalar kwakwalawarsu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China