in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Barazanar mutuwa da matan da suka taba haifuwa suke fuskanta ba ta kai wadanda ba su taba haihu ba
2017-09-22 08:11:46 cri

Wata kungiyar kasa da kasa ta kaddamar da rahoton nazarin ta a kwanan baya, inda suka nuna cewa, watakila haihuwa tana da alaka da barazanar mutuwar mata, sakamakon wasu cututtukan da ake yawan kamuwa da su. Adadi ya shaida cewa, irin wannan barazana da matan da suka taba haifuwar 'ya'ya suke fuskanta ba ta kai wadanda ba su taba haihu ba.

Masu nazari karkashin shugabancin kwalejin koyon kimiyya da fasaha na kasar Birtaniya sun yi nazari kan alakar da ke tsakanin batutuwan haihuwa, kamar haihuwar 'ya'ya, da shayar da 'ya'ya da nonon mahaifa mata, da kuma barazanar mutuwar mata sakamakon wasu cututtukan da ake yawan kamuwa da su, kamar ciwon sankarar mama, da shan inna, da kuma ciwon zuciya.

Masu nazarin sun tantance bayanan lafiyar mata fiye da dubu 320, wadanda suka fito daga kasashe 10 na Turai. Matsakaicin shekarun matan ya kai 50 a duniya. An dauki matsakaicin shekaru 12.9 ana gudanar da binciken kan ko wace mace. A cikin wadannan shekaru, wasu fiye da dubu 14 sun rasu, ciki had da wasu dubu 5 da dari 9 da 38 wadanda suka rasu sakamakon ciwon sankara, yayin da wasu dubu 2 da dari 4 da 4 suka rasu ne sakamakon ciwon kayayyakin ciki masu taimakawa gudanar jini.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, galibi dai, barazanar mutuwar matan da suka taba haihuwar 'ya'ya ba ta kai wadanda ba su taba haihu ba har da kashi 20 cikin dari. Ban da haka kuma, irin wannan barazana da wadanda suka shayar da 'ya'yansu da nononsu suke fuskanta ba ta kai wadanda ba su yi hakan ba.

Har ila yau, barazanar mutuwa sakamakon ciwon sankara da matan da suka taba haihuwar 'ya'ya suke fuskanta ba ta kai wadanda ba su taba haihuwa ba. Kana kuma irin barazana da wadanda suka taba haihuwar 'ya'ya biyu ko uku suke fuskanta ba ta kai wadanda suka haifi da ko 'ya daya kacal ba.

Haka lamarin yake a fannin barazanar mutuwar mata sakamakon ciwon kayayyakin ciki masu taimakawa gudanar jini.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, watakila tsarin sarrafa sinadaran Hormone da ke cikin jikin dan Adam shi ne dalilin da ya sa hakan. Haihuwar 'ya'ya, da shayar da su da nonon mahaifa mata da dai sauransu, suna sauya yawan sinadaran "Hormone" da ke jikin mata.

Amma duk da haka, masu nazarin sun ci gaba da cewa, sun samu sakamakonsu ne bayan da suka dudduba, tare da tantance bayanan. Don haka kada a ce, haihuwar 'ya'ya da kuma shayar da su da nonon mahaifa mata, suna iya rage barazanar mutuwar mata. Ana bukatar ci gaba da nazari a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China