in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mata masu fama da ciwon sukari sun fi saukin kamuwa da ciwon zuciya sakamakon gurbatar iska
2017-09-18 07:18:10 cri

Gurbatar iska, wani babban dalili ne da ke haddasa kamuwa da ciwon zuciya. Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya yi mana kashedi da cewa, ga alama mata masu fama da ciwon sukari sun fi saurin samun illa daga gurbatar iska. Wato dai idan irin wannan aji na mata suka dade suna kasancewa cikin iska gurbatacciya, hakan na barazana gare su ta fuskar karin yiwuwar samun cututtukan da suka shafi zuciya da magudanar jini.

Masu nazari daga jami'ar Harvard ta kasar Amurka, sun yi karin bayani da cewa, sun tantance shekarun mutane da haihuwa, tarihin iyalansu ta fuskar kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da magudanar jini,da nauyin jikinsu, al'adarsu na shan taba, da wuraren da suke zaune da dai sauran su. A karshe dai abun da ya wuce zato shi ne masu fama da ciwon sukari sun fi saukin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da magudanar jini.

Masu nazarin sun tantance bayanan da suka shafi lafiyar Amurkawa mata fiye da dubu 100, da kuma yadda suka kasance cikin gurbatar iska. Dukkan wadannan Amurkawa mata sun shiga wani nazari dangane da lafiyar mata cikin dogon lokaci. Daga shekarar 1989 zuwa ta 2006, wasu fiye da dubu 3 da dari 8 daga cikinsu, sun kamu da ciwon zuciya, yayin da wasu fiye da dubu 3 da dari 2 suka kamu da shan inna.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, bayan da dukkan wadannan Amurkawa mata da suka tantance bayanansu suka dade suna kasancewa cikin gurbatar iska, barazanar da suke fuskanta wajen kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya, da magudanar jini ta dan karu, amma wadanda suke fama da ciwon sukari sun fi fuskantar karuwar irin wannan barazana.

Ban da haka kuma, matan da shekarunsu suka wuce 70 da haihuwa, da kuma mata masu kiba sun fi saukin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da magudanar jini sakamakon gurbatar iska.

Amma duk da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, sun gudanar da nazarinsu ne kan mata masu farar fata tsoffi, da kuma masu matsakaicin shekaru kadai. Wato dai akwai bukatar zurfafa nazarin na su kan maza da kuma bakaken fata, masu rawayar fata da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China