in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yanayin bugun zuciya da ya sabawa al'ada yana iya haifar da barazana ga lafiyar mata
2017-09-11 14:52:39 cri

Wata kungiyar kasa da kasa ta kaddamar da sabon rahoton nazari ta a mujallar ilmin likitanci ta kasar Birtaniya, inda ta ce, in an kwatanta su da maza, mata wadanda yanayin bugun zuciyar su ya sabawa al'ada, na da karin barazana ta fuskantar ingancin lafiyarsu.

Masu nazari daga jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya, da takwarorinsu na kasashen duniya sun gama kansu wajen tantance nazarce-nazarce guda 30 masu alaka da hakan, inda suka tattara bayanan da suka shafi lafiyar mutane fiye da miliyan 4.

Sakamakon nazarin ya shaida mana cewa, idan yanayin bugun zuciya na mata ya saba da al'ada, mai yiwuwa su fuskanci kalubalen kamuwa da ciwon zuciya da shanyewar tsagin jiki sama da takwarorin su maza, kuma maganin da ake ba su wajen shawo kan yanayin bugun zuciyar ta su bai cika dacewa ba ko aiki yadda ya kamata, idan an kwatanta da tasirin sa a jikin takwarorin su maza masu fama da irin wannan matsala.

Masu nazarin sun yi karin bayani da cewa, watakila dalilin da ya sa hakan shi ne, kasancewar mata masu dimbin yawa ba sa samun isasshiyar jinya ta shawo kan matsalar yanayin bugun zuciyar su, in an kwatanta su da maza.

Hakika dai a halin yanzu akwai wasu nau'o'in magunguna na shawo kan matsalar yanayin bugawar zuciya. Idan masu fama da matsalar sun samu jinya yadda ya kamata kuma kan lokaci, to, mai yiwuwa ne su kaucewa kamuwa da shanyewar jiki, da sauran munanan cututtuka.

Wani kwararre daga asusun kula da zuciya na kasar Birtaniya ya bayyana mana cewa, watakila bambancin jikunan mutane na da tasiri game da yadda ake rigakafi da kuma shawo kan cutar rashin daidaitar yanayin bugawar zuciya, don haka kamata ya yi a yi la'akari da wannan yayin da aka tsara shirin ba da jinya. Nan gaba kuma, ana bukatar zurfafa nazari kan ainihin dalilin da ya sa ake samun irin wannan bambanci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China