in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Watakila mata na iya yin kiba idan suna barci a dakuna masu haske sosai
2017-09-03 17:16:19 cri

Matsalar kiba ba kawai tana da nasaba da yawan cin abubuwa fiye da kima,ko rashin isasshen barci ba, har ma watakila yin barci a dakunan da ke haske sosai na iya haddasa matsalar kiba ga mata. Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya gano cewa, dalilin da ya sa haka shi ne watakila domin haske yana kawo illa ga canjin wasu sinadarai a jikin bil-Adama.

A kwanakin baya masu nazari daga kwalejin nazarin ciwon sankara a birnin London na kasar Birtaniya sun kaddamar da wani rahoto dake nuna cewa, yayin da suke nazarin alakar da ke tsakanin ciwon sankarar mama da kuma matsalar kiba, sun gano illar da haske ke haifarwa mutane idan suna barci a dakunan dake da haske sosai.

Masu nazarin sun dauki shekaru 40 suna gudanar da bincike a kan matan kasar Birtaniya kimanin dubu 113. A cikin wannan nazari, sun raba karfin hasken da ke cikin dakunan da ake yin barci a ciki zuwa matakai guda 4, wato hasken da ake iya karanta littafi a cikin daki, hasken da ake iya ganin abubuwa a cikin daki, amma ba su dace da karanta littafi ba, hasken da ake iya ganin hannu a cikin daki, amma ba za a iya ganin dakin baki daya ba, da hasken da ba za a iya ganin komai ba a cikin dakin ba.

Masu nazarin sun gano cewa, idan mata sun yi barci a cikin dakunan da ke da haske, to, mizanin BMI na awon nauyin mutum a kilogiram a raba da tsayin mutum a mizanin sikwaya mita, tsawon kewayen kunkuminsu, daidaito tsakanin kunkumi da kwatangwalo, da daidaito tsakanin kunkuminsu da tsayinsu dukkansu sun fi na wadanda suke barci a cikin dakunan da babu haske sosai a ckinsu. Duk da cewa, an yi la'akari da al'adarsu ta motsa jiki, tsawon lokacin barci da dai sauransu, amma wadanda suke barci a dakunan da ke da haske sun fi wadanda suke barci a dakunan da ke da duhu kiba.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, haske yana illa ga yadda jikin dan Adam yake aiki, ta yadda yake iya illa ga canjin wasu sinadarai a jikin bil-Adama. Amma duk da haka ana bukatar ci gaba da nazari kan yadda haske yake kawo illa wajen canja wasu sinadarai a jikin bil-Adama. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China