in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba yana amfani ga lafiyar jijiyoyin jini
2017-08-14 07:14:01 cri

Wani sabon nazari ya nuna mana cewa, lafiyar jijiyoyin jini na mata Japanawa da suke kama halittun teku ta hanyar yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba, ta fi ta takwarorinsu wadanda ba sa yin hakan kyau. Hakan ya shaida mana cewa, watakila yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba yana amfani ga lafiyar jijiyoyin jini.

A wasu wurare da ke bakin teku a kasar Japan, wasu masu kama kifi mata na kama dabbobin teku na abinci ta hanyar yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin amfani da na'urar dauke da iskar Oxygen ba. Galibi dai sukan dauke numfashi har mintoci 2 zuwa 3 yayin alkafura cikin ruwa yayin da suke kama halittun teku. Tun da can dai, a wadannan wurare, mata mazauna wurin na yin nutso cikin ruwa, su kama halittun teku ba tare da yin amfani da na'urar dauke da iskar Oxygen a ciki ba, amma sakamakon ci gaban fasahar zamani ta kama kifi da ta kiwon halittun teku da dan Adam yake yi, ya sa yawan masu kama kifi mata da suke amfani da waccan dabara ta hanyar yin nutso cikin ruwa ba tare da yin amfani da na'urar ba yana raguwa a kai a kai. Mahukuntan Japan sun fara kiyaye irin wannan hanyar gargajiya ta kama kifi.

Wata kungiyar nazari ta kasar Japan ta yi nazari kan Japanawa mata 200 da matsakaicin shekarunsu ya kai 65 a duniya, ciki had da masu kama kifi mata 121 da suke kama halittun teku ta hanyar yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin amfani da na'urar dauke da iskar Oxygen ba. Masu nazarin sun gano cewa, lafiyar jijiyoyin jininsu ta fi ta takwarorinsu kyau.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini tana karuwa ne, sakamakon karuwar shekarun 'yan Adam a duniya. A baya, an san cewa, sassarfa, da ninkaya da dai irinsu, suna taimakawa wajen kyautata lafiyar jijiyoyin jini. Wannan sabon nazari da aka yi ya tono mana cewa, watakila yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba shi ma yana iya inganta lafiyar jijiyoyin jini. Masu nazarin sun yi fatan cewa, za su ci gaba da nazarinsu, a kokarin gano yadda yin alkafura cikin ruwa ba tare da yin numfashi ba yake yake kyautata lafiyar jijiyoyin jinin masu kama kifi mata na Japan, ta haka kuma za a iya kaiwa ga lalubo bakin zaren yin rigakafin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da jijiyoyi. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China