in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kila yin aikin dare na dogon lokaci zai iya dan kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya
2017-08-07 07:17:10 cri

Masu karatu, yayin da kuke fara barci da daddare, wasu kuma a lokacin suke fara aikinsu. To, ko mene ne illar da yin aikin dare yake kawo wa lafiyar dan Adam?. Masu nazari daga kasar Amurka sun kaddamar da sakamakon nazarinsu a kwannan baya, inda suka nuna cewa, yin aikin dare na dogon lokaci, zai iya dan kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya.

Kowa ya sani cewa, shan taba, da cin abinci ba yadda ya kamata ba, da rashin isasshen motsa jiki, da matsalar kiba da dai irinsu, su kan kara wa mutane barazanar kamuwa da ciwon zuciya. Amma a shekaru da dama da suka wuce, akwai sabani tsakanin masu ilmin likitanci dangane da barazanar kamuwa da ciwon zuciya wadda yin aikin dare yake haddasawa.

Sabili da haka ne masu nazari daga asibitin cututtukan da suka shafi mata na Brigham da ke kasar Amurka, suka tantance bayanan da suka shafi ma'aikatan jinya kimanin dubu 180 na kasar Amurka, wadanda suka dade suna aikin dare. Wadannan ma'aikatan jinya su kan yi aikin dare a kalla sau 3 ne a ko wane wata. A cikin shekaru 24 da aka yi binciken, ma'aikatan jinyar fiye da dubu 10 sun kamu da ciwon zuciya.

Duk da wasu dalilan da ake tsammanin cewa, suna kara barazanar kamuwa da ciwon zuciya, masu nazarin sun gano cewa, barazanar kamuwa da ciwon zuciya da ma'aikatan jinya mata da suka yi aikin dare fiye da shekaru 10 suke fuskanta, ta fi ta wadanda ba su yi aikin na dare ba da kashi 15 zuwa kashi 18 cikin dari.

Har ila yau kuma, karuwar barazanar kamuwa da ciwon zuciya tana karuwa idan an ci gaba da yin aikin dare tsawon lokaci a baya. Akasin haka kuma, ana iya rage wannan barazana ta kamuwa da ciwon zuciya idan aka kauracewa yin aikin na dare. Wannan dai lamarin ya shaida mana cewa, yin aikin dare yana kawo wa mutane barazanar kamuwa da ciwon zuciya, amma ana iya yin kandagarkin hakan.

Masu nazari daga asibitin cututtukan da suka shafi mata na Brigham da ke kasar Amurka wadanda suka gudanar da nazarin sun yi nuni da cewa, hukuncin da suka yanke cikin nazarinsu, ya yi daidai da hukuncin da aka yanke cikin nazarce-nazarcen da aka gudanar a baya. Wato watakila barazanar kamuwa da ciwon zuciya da ake fuskanta, za ta sha bamban sosai bisa mabambantan tsarin aikin dare, a lokuta daban daban. Don haka ya zama wajibi a ci gaba da yin nazari kan alakar da ke tsakanin tsarin aiki a lokaci daban daban, da halin musamman na ko wane mutum, da kuma lafiyar zuciyar sa. (Tasallah Yuan).

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China