in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Batutuwa guda 10 dangane da ciwon sukari (A)
2017-07-17 08:30:09 cri

A shekarun baya, yawan wadanda suka fama da ciwon sukari ya samu saurin karuwa a duk fadin duniya. Duk da haka jama'a ba su san ciwon na sukari sosai ba, suna da rashin fahimta kan wannan ciwo. A cikin shirinmu na wannan mako da na mako mai zuwa, zan yi bayani kan wasu batutuwa dangane da ciwon na sukari.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi karin bayani kan shafinta na yanar gizo ta Internet da cewa, yanzu yawan masu fama da ciwon sukari ya karu zuwa miliyan 422 a shekarar 2014 daga miliyan 108 a shekarar 1980 a duk fadin duniya, kuma yawancinsu na zama ne a kasashe masu tasowa.

Yanzu haka ciwon na sukari yana yaduwa a duk duniya baki daya. A duniyarmu, yawan wadanda suka kamu da ciwon, kuma shekarunsu suka wuce 18 ya karu zuwa kashi 8.5 cikin dari a shekarar 2014, daga kashi 4.7 cikin dari na shekarar 1980. Abun da yake addabar mutane shi ne ya zuwa yanzu yawan wadanda suka kamu da ciwon na sukari yana ta karuwa.

A shekarar 2012 da ta gabata, mutane kimanin miliyan 1 da dubu 500 ne suka rasu sakamakon ciwon sukari a fadin duniya, yayin da dimbin sukari da ke jinin dan Adam ya kara wa mutane barazanar kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini da dai sauransu, lamarin da ya zama sanadiyyar mutuwar mutane kimanin miliyan 2 da dubu 200. Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta yi hasashen cewa, ya zuwa shekarar 2030, ciwon sukari zai kasance muhimmin dalili na 7 da zai zama sanadin mutuwar dan Adam.

Ban da haka kuma, hukumar WHO ta kaddamar da wani rahoto dake cewa, mutanen da suka rasu sakamakon ciwon sukari, wadanda yawansu ya wuce kashi 80 cikin dari na zaune ne zama a kasashe masu karancin kudin shiga. A kasashe masu sukuni, yawancin masu fama da ciwon sukari sun yi ritaya, amma a kasashe maso tasowa, shekarun yawancin masu fama da ciwon sukari ya wuce 35 amma bai kai 64 ba, lamarin da ya haddasa babbar illa ga lafiyar al'umma da bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'umma.

Akwai nau'o'in ciwon sukari guda 2, wato na farko da na biyu. Masu fama da ciwon sukari mai nau'I na 1 ba su iya samar da sinadarin Insulin da kansu, dole sai an yi musu allurar sinadarin Insulin domin su rayu. Masu fama da ciwon sukari mai nau'I na 2 kuma, suna iya samar da sinadarin Insulin da kansu, amma ba isasshe ba, ko kuma jikinsu ba ya iya sarrafa sinadarin yadda ya kamata. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China