in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ilmin ciwon sukari (B)
2017-07-09 11:17:49 cri

A shekarun baya, yawan wadanda suka fama da ciwon sukari ya samu saurin karuwa a duk fadin duniya. Duk da haka jama'a ba su san ciwon na sukari sosai ba, suna da rashin fahimta kan wannan ciwo. A cikin shirinmu na makon jiya, na musunta bayanai guda 2, wato babu bukatar a mai da hankali sosai kan ciwon na sukari, kuma ana iya shawo kan ciwon sukari baki daya ta hanyar cin abinci kawai. A wannan mako, zan ci gaba da yin bayani kan wata tambaya ta daban dangane da ciwon na sukari.

Jama'a suna tsammanin cewa, kada masu fama da ciwon sukari su ci ko wane irin sukari. Don haka, wasu sun tsara shirin girke-girke mai kiwon lafiya, inda suka yi shelar cewa, kada masu fama da ciwon sukari su ci shinkafa, burodi da dai ire-irensu, nama da 'ya'yan itatuwa.

Masu ilmin likitanci ba su yi na'am da irin wannan shirin girke-girke ba. Suna ganin cewa, ya zama tilas a samu daidaito yayin da masu fama da ciwon sukari suke cin abinci, a tabbatar da samun daidaito a tsakanin mabambantan sinadarai masu gina jiki. Alal misali, kamata ya yi masu fama da ciwon sukari su ci shinkafa, ko burodi ko sauran irinsa da yawansu ya wuce giram 150, amma bai kai giram 200 ba.

Bayan haka kuma, idan masu fama da ciwon sukari ba su ci isashen nama ba, to, zai kawo illa ga lafiyarsu, alal misali, rashin isasshen furotin a jikinsu ya kan raunana karfinsu na yaki da cututtuka.

Dangane da 'ya'yan itatuwa kuma, yadda 'ya'yan itatuwa suke da zaki, ko a'a ya dogara da yawan sukari da ke cikinsu. Jikin dan Adam ba shi bukatar sinadarin Insulin wajen sarrafa sukarin da ke cikin 'ya'yan itatuwa. Idan yawan sukari da ke jinin masu fama da ciwon sukari ya yi kasa da 10 bayan cin abinci, za su iya cin wasu 'ya'yan itatuwa. Lokaci mafi dacewa da cin 'ya'yan itatuwa shi ne tsakanin karya kumallo da abinci rana, ko kuma tsakanin abincin rana da abincin dare.

Ban da haka kuma, ya kamata masu fama da ciwon sukari su sarrafa yawan sukari da ke jininsu ta hanyar kimiyya cikin dogon lokaci kuma yadda ya kamata. Kada su rage yawan sukari da ke jininsu da yawa cikin gajeren lokaci. Saboda yawan raguwar sukari da ke jinin masu fama da ciwon ko kuma saurin raguwar yawan sukari da ke jininsu fiye da kima ya kan haddasa hauhawar yawan sukari da ke jininsu cikin gajeren lokaci. Rage yawan sukari da ke jinin masu fama da ciwon sukari da yawa cikin gajeren lokaci bai cancanci yadda jikinsu yake aiki ba,mai yiwuwa ne zai haifar da mummunan sakamako. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China