in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bugun yara a tuwon duwawu yana tasiri ga tunaninsu
2017-06-27 13:30:14 cri

Wasu iyaye sun yi shelar cewa, yara ba sa jin magana sai an buge su,. Ranar 30 ga watan Afrilu na ko wace shekara, rana ce ta yaki da bugun yara ta duniya. Kasar Amurka ta kaddamar da wani sakamakon nazari da aka kwashe shekaru 50 ana gudanar da shi, inda aka gano cewa, yiwa yara tarbiya ta hanyar bugunsu a tuwon duwawu, ko kadan bai dace ba. Kuma, hakan ya kan sa yara su fandare har ma ya kara musu barazanar kamuwa da ciwon tunani.

Masu nazari daga jami'o'in Michigan da Texas ta kasar Amurka su ne suka gudanar da wannan nazari cikin hadin gwiwa a kan mutane kimanin dubu 160. Sa'an nan masu nazarin sun bambanta yadda aka bugi kananan yara a tuwon duwawu da kuma yadda aka gana musu azaba.

Masu nazarin daga jami'ar Texas ta kasar Amurka sun yi nuni da cewa, dalilin da ya sa iyaye suke yiwa 'ya'yansu tarbiya ta hanyar bugunsu a tuwon duwawu shi ne domin suna fatan 'ya'yansu su yi musu biyayya, amma sakamakon nazarinsu ya bankado cewa, bugun kananan yara a tuwon duwawu ba zai haddasa kome ba, sai illa kawai.

Nazarin ya shaida cewa, idan aka ci gaba da bugun yaro tun yana yaran takarsa, mai yiwuwa ne hakan ya sa yaron ya rika aikata wasu munanan dabi'un da suka sabawa kyakkyawar zamantakewa bayan da ya girma, sa'an nan zai kara fuskantar barazanar kamuwa da ciwon tunani. Har ila yau kuma, irin wadannan mutane su kan bugi 'ya'yansu, lamarin da ya tabbatar da wani bayanin da ke cewa, ana gadar yadda ake tarbiyar yara ta hanyar bugun su daga zuriya zuwa zuriya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, galibi dai ana ganin cewa, akwai babban bambanci a tsakanin bugun kananan yara a tuwon duwawunsu da kuma gana wa kananan yara azaba a wasu sassan jikinsu da gangan, amma nazarin da suka gudanar ya shaida cewa, lamarin ba haka yake ba! Illar da bugun kananan yara a tuwon duwawu take haifarwa kan kananan yaran ta kusan yi daidai da illar da gana musu azaba take haddasawa, amma ba ta da tsanani sosai.

Yanzu bugun kananan yara a tuwon duwawu ya zama ruwan dare gama duniya. Asusun kula da kananan yara na MDD wato UNICEF ya taba kaddamar da wani rahoto a shekarar 2014, inda ya ce, kashi 80 cikin na iyayen a duniya sun taba bugun 'ya'yansu a tuwon duwawu. A kasar Amurka, yawan wadanda suka amince sun bugi 'ya'yansu a tuwon duwawu ya dan ragu a shekarun baya. Yanzu ana ilimantar da jama'a game da adawa da bugun kananan yara a tuwon duwawu a duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China