in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wadanda suke da kanne maza ko mata ba safai su kan yi kiba ba
2017-06-05 09:51:27 cri

A cikin wani iyali mai yawan yara, a wasu lokuta, babba bai jin dadin halayyar kannensa maza ko mata ba, saboda yadda su kan lalata abubuwansu na wasa, ko kuma su kan kawo wa wansa ko yarsa matsala. Sakamakon nazari da aka gudanar a kasar Amurka ya shaida cewa, samun kanne maza ko mata yana iya taimakawa wajen kiyaye daidaiton nauyin jikin mutum.

Masu nazari sun zabi kananan yara 697 na kasar Amurka, tare da yin bincike kan nauyin jikinsu ke sauyawa tun daga haihuwarsu har lokacin da suka kai shekaru 6 a duniya.

Alkaluma sun shaida cewa, nauyin jikin kananan yara da shekarunsu suka kai 6 a duniya, amma ba su samu kanne maza ko mata ba, ya kan wuce misali cikin sauki. Yiwuwar samun kiba da suke fuskanta ta ninka sau 3 gwargwadon wadanda suke da kanne yayin da shekarunsu suka kai 3 ko 4 a duniya.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu bai nuna cewa, tabbas ko 'ya daya tak a gida ta kan samu kiba ba. A'a! Watakila kara samun da ko 'ya a gida yana iya taimakawa wajen kiyaye kiban sauran yara a gidan.

Masu nazarin sun yi karin haske da cewa, dalilin da ya sa haka shi ne watakila domin yara manya suna kara nuna himma bayan da suka samu kanne ko kanwa. Alal misali, yara manya su kan kara yin wasa tare da kannensu maza ko mata wadanda suka fara koyon yin tafiya. Ban da haka kuma, bayan haihuwar jarirai, iyaye suna kara zuwa wurin shan iska tare da yaransu, ta haka yara manya su na kara yawan zama wajen kallon TV.

Har ila yau a wasu lokuta, iyayen da ko 'ya daya tak a gida su kan mai da hankali kan yadda 'ya'yansu suke cin abinci fiye da kima, su kan nemi 'ya'yansu su kara cin abinci, hakan watakila zai sanya 'ya'yansu su kara fuskantar barazanar yin kiba.

Amma bayan samun kani ko kanwa a gida, kila iyayen bas a mayar da da hankali fiye da kima kan yadda 'ya'yansu manya suke cin abinci, ta haka manyan yaran su kan iya kyautata yadda suke cin abinci da kansu. A cikin irin wannan iyali, yara su kan kiyaye daidaiton nauyin jikinsu yadda ya kamata, gwargwadon wadanda ba su da kani ko kanwa.

Duk da haka, masu nazarin sun yi nuni da cewa, yayin da suke gudanar da nazarinsu, ba su yi la'akari da illolin da wasu dalilai suka haifar kan nauyin jikin yara ba, kamar yadda iyaye ke rabuwa da mazajensu, ko sun rasa aikin yi, ko sun kaura zuwa wasu wurare. Hakika dai, akwai dalilai da dama da suka haddasa illa ga kiban yara, alal misali, nauyin jikin iyayensu, yadda iyaye mata suka shayar da su nono, yadda suke yin barci da kuma farkawa daga barci, yadda suke motsa jiki kullum da dai sauransu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China