in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shawarar "Ziri daya hanya daya" ta zo a daidai kan gaba
2017-05-31 09:46:13 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI

Tare da fatan daukacin ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda na ke lafiya a nan birnin Kano.

Kodayake, kimanin makonni biyu kenan da kammala taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa bisa shawarar "Ziri daya hanya daya" a birnin Beijing. Amma duk da haka ina iya tuna irin muhimmancin da wannan taro ke da shi wajen kokarin ganin an hada karfi da karfe domin fuskantar kalubaloli da dama da suka zamanto tamkar 'dan zane, mai wuyar daurawa ga kasashen duniya.

Hakika, ya zama wajibi a jinjinawa kasar Sin dangane da wannan hangen nesa da ta yi, inda ta gano cewa, lalle sai fa an gudu tare ne a ke iya tsira tare. Wato ba za a taba iya tunkarar matsalolin da suka dabaibaye duniya ba, har sai kasashen duniya sun dunkule sun zama tsintsiya daya. Lamarin da za a iya cewa, ya haska irin bukatar da a ke da ita na samar da shiri irin "Ziri daya hanya daya" a daidai wannan gaba da kasashen duniya ke fama da matsaloli irin iri, kama dagashakkunsulin arziki, matsalar tsaro, da na rashin wadatar ababen more rayuwa, dai sauransu.

Kodayake, wasu kasashe suna nuna shakkunsu dangane da wannan shiri na 'Ziri daya hanya daya' bisa tunanin wai kasar Sin ta fake da wannan shiri ne domin ta kankane harkokin tattalin arzikin duniya. Amma zahirin gaskiya ba haka lamarin ya ke ba, kasar Sin tana son a gudu tare ne kuma a tsira tare. Domin tarihi ya tabbatar da cewa, babu wata kasa a duniya da ta samu bunkasuwa ita kadai ba tare da yin cudanya da sauran kasashe ba.

Dangane da haka, yana da muhimmancin gaske ga sauran kasashen duniya su rungumi wannan shiri na 'Ziri daya hanya daya' da zuciya daya, duba da cewa, kimanin kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 68 sun Riga sun amince da tanade tanaden hadin gwiwar wannan shiri na 'ziri daya hanya daya'. Kazalika, saurin bunkasar tattalin arziki da kasar Sin ta samu wanda har yanzu ke jan hankalin duniya wani kyakkyawan misali ne na irin tasirin da yin hadin gwiwa da cudanya ke haifarwa wajen habaka tattalin arziki, sakamakon yadda kasar Sin ta bude kofofin ta gami da kulla yarjeniyoyin hadin gwiwa da kasashen ketare da dama.

Ya kamata, al'ummar duniya su fahimci cewa, babu wata manufa maras kyau dangane da shawarar 'Ziri daya hanya daya', illa kokarin ganin an hada kai domin zama tsintsiya daya wajen tunkarar matsalolin da suka zamanto na bai daya tsakanin kasashen duniya, ga misali, karancin ababen more rayuwa, durkushewar tattalin arziki, karancin makamashi, da tabarbarewar harkar tsaro, rashin aikin yi ga dimbin al'umma, da dai sauran matsaloli.

Ina fatan kafin shekarar 2019 lokacin da aka tsayar da kudurin gudanar da taro na gaba kan wannan batu, adadin kasashen da za su amince da shirin za su karu.

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China