in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sanya abun toshe kunnuwa a yayin taron rera wakoki yana iya kiyaye kunnuwan mutane
2017-05-24 07:04:47 cri

Wata kila a ganin matasa, sanya abun toshe kunnuwa a yayin taron rera wakoki ba shi da ma'ana. Amma wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Holand ya nuna cewa, sanya abun toshe kunnuwa a yayin taron rera wakoki, yana taimakawa wajen hana amo mai kara bisa ma'aunin Decibel ya raunana kafar ji ta mutane.

A shekarun baya bayan nan, yawan wadanda suka gamu da matsalar sauraro yana ta karuwa, lamarin da yake addabar kasa da kasa. Daya daga dalilan da suka haddasa hakan shi ne karar da mutane suke saurara, yayin da suke gudanar da harkokin nishadi wadda take ta karuwa. Alal misali, taron kide-kide ko taron rera wakoki da dai sauransu.

Masu bincike a jami'ar Utrecht ta kasar Holand sun tattara masu aikin sa kai 51, wadanda matsakaicin shekarunsu suka wuce 27 a duniya a birnin Amsterdam, inda suka gayyace su halartar wani taron rera wakoki na tsawon awoyi 4 da rabi. A yayin taron, wanda matsakaicin karfin amo ya kai 100 bisa ma'aunin Decibel, wasu 25 sun sanya abubuwan toshe kunnuwa, yayin da wasu 26 ba su sanya ba.

Sakamakon binciken iya saurararsu bayan taron rera wakokin, ya shaida cewa, mutanen da yawansu ya kai kashi 8 cikin dari daga cikin masu sanya abun toshe kunnuwa, sun gamu da matsalar ji cikin gajeren lokaci, yayin da mutanen da yawansu ya kai kashi 42 cikin dari daga cikin wadanda ba su sanya abun toshe kunnuwa ba, suka gamu da wannan matsalar.

Ban da haka kuma, mutanen da yawansu ya kai kashi 12 cikin dari, daga cikin masu sanya abun toshe kunnuwa sun gamu da matsalar ji a kunnen su, yayin da mutanen da yawansu ya wuce kashi 40 cikin dari daga cikin wadanda ba su sanya abun toshe kunnuwa ba suka gamu da matsalar.

Masu nazarin daga jami'ar Utrecht ta kasar Holand din sun yi bayani da cewa, nazarinsu ya kara tabbatar da yadda abubuwan toshe kunnuwa, suke hana yin asarar ji cikin gajeren lokaci, a yayin taron rera wakoki da sauran wuraren nishadi. Don haka suka ba da shawarar cewa, ya kamata a karfafa gwiwar mutane, da kuma yayata amfani da abun toshe kunnuwa, a kokarin hana yin asarar ji sakamakon kara.

Galibi dai, karfin amo da na'urar sitiriyo da ake amfani da su a gida ke samarwa, ba ya wuce lamba 100 bisa ma'aunin Decibel, yayin da karfin amon hirar da ke tsakanin mutane ya kan wuce lamba 40, amma baya wuce 60 bisa ma'aunin na Decibel. Amma karfin amo da ake ji a kujerun gaba, yayin taron rera wakoki ya kan wuce 120, ko sama da 60 bisa ma'aunin Decibel. Amon da karfinsa da ya wuce 127 bisa ma'aunin Decibel, ya kan sanya mutane su ji kara cikin kunne, yayin da adadin da ya kai 141, kan sa mutane ya ji tashin zuciya, tare da yin asarar jin sa nan take. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China