in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin mr. Wang Yi a wasu kasashenmu na Afirka guda 4 ta ja hankalina sosai
2017-05-18 18:06:28 cri
A ranar 19 zuwa 23 ga watan Mayun shekarar 2017 ne, shehun malami ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi zai fara wata ziyara a wasu kasashenmu na Afirka su 4 da suka hada da kasashen Cape Verde, Mali, Cote d'ivoire da kasar Maurtania. Wannan muhimmiyar ziyara mai tarishi, a nawa ra'ayin wani mataki ne kasar Sin ta dauka a cikin shekarar 2017 dan kyautata huldarta da kasashenmu na Afirka masu tasowa, kana hakan zai kara zaburar da bunkasuwar tattalin arzikin kasashenmu na Afirka masu tasowa zuwa wani saban mataki na koli mai tagomashi da yalwatuwa ga nahiyarmu ta Afirka.

Muna godiya ga mahukuntan kasar Sin, muna godiya ga ministan harkokin ketare na kasar Sin Wang Yi a bisa wannan ziyara ta sada zumunci da kauna da ya kawo mana a nahiyarmu ta Afirka. Muna fatan sauran kasashe takwarorin kasar Sin za su hanzarta yin koyi da kasar Sin wajen bada muhimmanci ga bunkasuwar Afirka, da kuma yaukakar zaman lafiya a kasashenmu na Afirka masu tasowa.

Daga Alhaji Ali kiraji Gashua,

Jihar Yobe

Tarayyar Najeriya

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China