in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmancin ganawa tsakanin shugaba Xi Jinping da shugaban kasar Amurka Donald Trump
2017-04-08 13:47:16 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Gaisuwa mai yawa tare da fatan alheri da fatan daukacin ma'aikatan ku suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya a nan birnin Kano. Ina farin cikin shaida muku cewa, na samu ikon sauraron sabon shirin ku na 'Gani Ya Kori Ji' na ranar Laraba 5 ga wata, wanda malamai Saminu Alhassan da Ahmad Fagam suka tattauna dangane da ganawar shugaba Xi Jinping da shugaba Donald Trump.

Hakika, dangantaka tsakanin kasashen Sin da Amurka na da dogon tarihi game da tasiri ga bangarorin biyu musamman yadda kasashen ke ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa tattalin arzikin juna. Kodayake, bambance bambancen dake tsakanin wadannan manyan kasashe a bayyane yake, musamman kan batun tankin Taiwan, da takaddamar tekun kudancin da batun zirin Koriya da dai sauransu. Duk da haka, sharhin da malamai suka yi ya kara haska irin hadin gwiwar dake tsakanin wadannan manyan kasashen biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya da kuma dangantar ciniki da ta kasuwanci mai tasiri dake tsakanin su.

Ba shakka, idan an dubi tarihin dangantaka tsakanin kasashen Sin da Amurka za a fahimci cewa, dangantaka ce mai karfi duba da yadda manyan shugabannin kasashen biyu su kai ta gudanar da ziyarar juna cikin shekaru gomai. Wato tun daga ziyarar aiki da shugaban Amurka Richard Nixon da uwargidan sa suka kawo kasar Sin a shekarar 1972 da ziyarar jagoran sake fasalta tsarin tattalin arzikin kasar Sin wato marigayi Deng Xiaoping zuwa Amurka a shekarar 1978 da ziyarar da ta biyo bayan haka wacce shi ma shugaban Amurka na wancan lokaci Jimmy Carter ya kawo kasar Sin.

Wata ziyara da ba za a manta da ita ba ita ce, ziyarar shugaban Amurka mai farin jini wato Bill Clinton da uwargidan sa Hillary tare da 'yar su Chelsea suka kawo kasar Sin a shekarar 1996, wanda bayan birnin Beijing shugaban ya samu ziyartar birnin Xi'an, inda ya leka makeken kabarin sarki Qin Shihuang wanda ya shahara a duniya. A baya bayan nan, ba za a manta da ziyarar da shugaban kasar Sin Xin Jinping ya kai ga takwaran sa na Amurka ba wato shugaba Barrack Obama a shekarar 2015 wacce za a ce ta yi tasiri sosai wajen dinke Barka da sauran bambance bambance dake tsakanin kasashen.

A halin yanzu, wannan ganawa ta kwanaki biyu da shugabannin su ka gudanafatanarin Mar-a-Logo dake jihar Florida ta ja hankalin masharhanta duba da cewa, tasirin kasar Sin ga bunkasar tattalin arzikin duniya na kara fito wa fili musamman yadda sabbin alkaluma suka bayyana irin yadda kasar Sin ta taimaka wa bunkasar tattalin arzikin duniya da kashi 30 cikin 100 a shekarar bara. Ba shakka, wannan ka iya zama makasudin kokarin kasar Amurka na kara kyautata dangantaka tare da hadin gwiwa da kasar Sin ta fannoni da dama da suka shafi tattalin arziki, da tsaro, muhalli, cinikayya da dai sauran su.

Hakika, kyautatuwar dangantaka tsakanin wadannan manyan kasashe zai haifar da alheri mai yawa ga sauran kasashen duniya, akasin haka kuwa, ba zai taba haifar da da mai ido ba. Domin Bahaushe kan ce, "idan giwawe biyu na fada to lalle ciyawa ce ke dandana kudarta". Dangane da haka, ina fatan wannan ganawa za ta taimaka wajen kara kyautata huldar dangantaka tsakanin kasashen Sin da Amurka.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China