in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta samu ci gaba a fannin cinikayya ta yanar gizo da amfani da motocin zamani
2017-03-07 09:00:51 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan daukacin ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing. Ina farin farin cikin shaida muku cewa, na samu zarafin sauraron sabon shirin ku na (Gani Ya Kori Jiki) dangane da siyan kaya ta hanyar yanar gizo wanda ku ka gabatar ranar 22 ga watan Fabrairu, amma ta shafin ku na yanar gizo bayan na kuskure saurara ta hanyar rediyo. Haka nan, na samu ikon sauraron wani sabon shirin (Gani Ya Kori Ji) na ranar 1 ga watan Maris, wanda malamai suka tattauna shirin gwamnatin kasar Sin na samar da karin cibiyoyin caji ga motoci masu aiki da lantarki domin bukatar irin wadannan motoci na zamani kimanin miliyan biyar nan da shekara ta 2020.

Hakika, wannan ya bayyana irin gagarumin sauyin da kasar Sin ke ci gaba da samu ta fannin kimiyya da fusaha da zamantakewa, domin idan an dubi yadda cinikayya ta hanyar yanar gizo ta samu karbuwa sosai ga miliyoyin al'ummar Sinawa, alama ce da ke haska irin yadda sha'anin ba da hidima ke kara samun gindin zama a fagen tattalin arzikin kasar Sin. A shekarar da ta gabata ta 2016 fannin bayar da hidima wanda ya hada da fannin cinikayya ta hanyar yanar gizo ya taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin yadda ya kamata, lamarin dake kara bayyana ci gaban da kasar Sin ta samu a wannan fanni. Musamman idan an yi la'akari da cewa, kasuwar cikin gida ta kasar Sin kadai wata hamshakiyar kasuwa ce duba cewa yawan al'ummar Sinawa ya zarce biliyan daya. A daya hannun kuma, kamfani mafi girma kuma mafi shahara a fannin cinikayya ta yanar gizo wato Alibaba na kasar Sin ne. Wannan shi ke ya kara tabbatar da cewa, kasar Sin na daf da kankane hada hada da cinikayya ta hanyar yanar gizo a fadin duniya. Domin hatta a nan Nijeriya, mutane da dama suna siyan kayayyaki daga ketare ta hannun kamfanin Alibaba. Saboda haka, gudunmawar da kamfanin Alibaba ke bayarwa a wannan fanni na cinikayyar yanar gizo ta zamani wani bangare ne na irin rawar azo a gani da kasar Sin ta ke takawa a fannin bunkasa tattalin arzikin duniya.

Dangane da batun shirin samar da karin cibiyoyin cajin motoci masu aiki da lantarki wanda zai wadatar da motoci kimanin miliyan 5 a fadin kasar Sin nan da shekara ta 2020, kamar yadda hukumar kula da makamashi ta kasar ta shelanta, za a iya cewa, wannan wani yunkuri ne dake nuna yadda kasar Sin ta dauki azamar cika sharuddan da yarjeniyoyin kare muhalli suka tanada ta hanyar rage fitar da hayaki mai guba da kuma rungumar tsarin makamashi mai tsafta. A ra'ayi na, wannan yunkuri zai iya gamsar da kungiyoyin dake fafutukar kare muhalli da sauran hukumomin da abin ya shafa cewa, lalle kasar Sin ta kuduri aniyar kyautata muhallin ta da ma duniya baki daya.

Ba shakka, samar da wadatattun cibiyoyin caji ga motoci masu aiki da lantarki na daga cikin kokarin da kasar Sin ke yi na cimma burin samar da dawamammiyar iska mai tsafta musamman a yankin arewacin kasar dake fama da matsalar gurbacewar iska a halin yanzu. A sa'i daya kuma, yunkurin yana bayyana yadda kasar ta Sin take martaba yarjeniyoyin kasa da kasa da suka shafi kare muhalli.

Dangane da haka, ya zama wajibi a yabawa kasar Sin bisa wannan bajinta na yunkurin samar da dubban cibiyoyin cajin motoci na zamani cikin kankanin lokaci, da kuma ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fannin cinikayya ta yanar gizo a cikin gida da ma kasashen ketare. Lamarin dake taimaka wa kananan kamfanoni da 'yan kasuwa samun damar shiga a dama da su a fagen kasuwancin zamani.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China