in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fatan alheri akan taruka biyu na 2017
2017-02-23 14:49:39 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI Beijing,

Bayan gaisuwa mai tarin yawa da fatan dukkanin ma'aikatan sashen Hausa na CRI suna cikin koshin lafiya. Ina son yin amfani da wannan dama in jinjinawa gwamnatin kasar Sin akan yadda take tafi da tsare tsarenta na tafi da gwamnatin, da alummatta da kuma muamula da kasashen duniya. Sannan tarukan da suka gabata a baya sun sami nasara sosai, ina fatan wannan za'a sami gagarumar nasara kamar a baya. Ina fatan a wannan taruka guda biyu na wannan shekara, gwamnatin kasar Sin zata ci gaba da manifofinta na kyautata rayuwar alummarta da rage talauci, da magance gurbacewar muhalli, da tunkarar dukkan wani kalubale da bunkasa masana'antu da kyautata muamula da kasashen duniya musammam na Afirka, da dai sauransu.

Ina yi muku fatan alheri.

Na gode Wassalam,

Abdulkadir Ibrahim,

Great Wall CRI Listeners Club,

Kano State,

Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China