in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taruka biyu na NPC da CPPCC na shekarar bana(2017) sun ja hankalina sosai
2017-02-20 15:01:41 cri
Salam Alaikum. Ina fata kuna nan lafiya, amin.

Ra'ayina game da muhimman taruka 2 na NPC da CPPCC na shekarar bana(2017), yana da kyau wakilan jama'ar kasar NPC da zaunannen komitin bada shawara na kasar Sin CPPCC su kara maida hankali ga batutuwan yaki da fatara da talauci a tsakanin jama'ar kasar Sin, kana su sa kaimi ga yaki da cin hanci da karbar rashawa a tsakanin kanana da manyan jami'an gwamnatin kasar Sin. Dud da cewar, wadannan batutuwan da na zaiyana suna daya daga cikin muhimman shawarwarin da aka gabatar wa gwamnati yayin taron taruka 2 na shekarar bara(2016), amma yana da kyau a kara jaddada su, ta yadda kwalliya za ta biya kudin sabulu.

Babu yadda za a yi gwamnati su iya yakar laifukan cin amanar kasa irinsu karbar cin hanci da rashawa a harkokin gudanarwar gwamnatin kasa, kana a iya yaki da aiyukan ta'addanci a samu galaba, matukar ba a dauki kwararan matakai da suka dace ba. Dole ne, mahukuntan birnin Beijing na kasar Sin su kara fito da muhimman tsare-tsare da za su rage tazarar rayuwa dake akwai tsakanin masu mulki da talakawan kasar Sin. Kana wakilan jama'ar kasar Sin(NPC) da zaunannen komitin bada shawara na kasar Sin(CPPCC) su gabatar da bukatar kara samar da aiyukan yi ga jama'ar kasar Sin wanda yin hakan zai agaza wa gwamnatin kasar Sin a yakin da suke yaki da ta'addanci, musamman ma a yankunan da ake kara samun karuwar 'yan ta'adda a kasar Sin.

Kana wakilan jama'ar kasar Sin da zaunannen komitin bada shawara na kasar Sin su gabatar da shawarar magance ta'azzarar matsalolin dake gurbata muhilli, masamman ma yadda matsalar ke damun jama'ar birnin Beijing da sauran sassan kasar Sin. Haka nan a kara bada kulawa ga tsofaffi a kasar Sin.

Ban da wannan, ina yaba wa mahukuntan kasar Sin bisa sabbin matakan yaki da cin hanci da karbar rashawa da suka dauka a shekarar bara ta 2016, inda gwamnatin kasar Sin suke kamo duk wanda ya gudu zuwa kasashen ketare dan kaucewa hukunci bisa laifukan cin amanar kasa(karbar cin hanci) daya aikata.

Daga

Alhaji Ali kiraji Gashua,

Jihar Yobe,

Najeriya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China