in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar Rediyo Ta Duniya a shekara ta 2017
2017-02-15 13:33:16 cri
A ranar 13 ga watan 2 a kowace shekara, rana ce ta ranar rediyo ta duniya, wadda MDD ta ayyana a matsayin ranar Rediyo ta duniya tun a shekara ta 2011.

Ba shakka a duniya akwai gidajen radiyo da dama da suka yi fice wadanda suka hada da na kasashen waje kamar su kasashenmu na Afrika asiya turai da amerika, misali a kasashe mu na Afrika akwi gidajen rediyon kasata Nigeria kamarsu Rediyon Nigeria Kaduna, Rima radio a sokoto, haka ma radiyo amfani dake jamhuriyar Niger, har wa yau a kasashen waje akwai gidajen redio kamar su BBC hausa, VOA hausa, Redion farance, Rediyon Canada, da kuma uwa uba Gidan Rediyon kasar Sin mai suna CRI wanda nake son in yi magana akansa.

A ko da yaushe, gidajen redio wurare ne dake bayar da dama ga jama'a domin sanar da su irin wainar da ake toyawa a duniya ta kowane fanni na rayuwar Dan Adam, misali idan muka dauki Gidan rediyon CRI tasha ce ta rediyo mai samar da labaru da dumi-duminsu, wadanda ke tsage gaskiya komi dacinta tare da sanar da mai sauraron irin abubuwan dake faruwa a kasar Sin da Afrika da ma duniya baki daya. Ba shakka idan ba da gidan rediyon CRI ba da ko shakka babu wadansu al'umma da ba su san kasar Sin ba, wannan tashar rediyo ta taimaka ainun wadda sada kasar Sin da sauran yankuna na ilahirin duniya, ta fannoni da dama wanda ya zamu sanadiyar bunkasuwar kasashen duniya da kasar Sin baki daya.

Akwai wadansu abubuwa da gidan rediyon CRI ya samar a kasar Sin da ma duniya kamar haka.

1. Gidan rediyon CRI ya bada gudunmuwa wajen samar da labarun kasar Sin ga kasashen duniya wanda ya kawo al'ummar kasashen nahiyoyi suka san kasar Sin ciki da waje.

2. Gidan rediyon CRI ya samar da cikakkiyar dangantakar kasuwanci tsakanin Sin da kasashen ketare wajen samar da shiraruwanda masu alaka.

3. Gidan rediyon CRI ya bada gagarumar gudunmuwa wajen samar da ingantattun shiraruwa domin kula dangantakar al'adu da yawon shakatawa ga al'ummar duniya.

4. Rediyon Kasar Sin CRI ya taka muhimmiyar rawa wajen samar da cikakkun bayanai akan jam'iyyar kwaminis JKS ta kasar Sin wajen yayata manufofinta tare da al'ummar kasar Sin da shuwagabannin Kasar sin bakidaya.

4.Rediyon CRI ya bayar da cikakkiyar dama wajen samar da labaru da dimi-diminsu ta fannin samar da tallafi ga kasashe masu tasowa musamman kasashenmu na Afrika.

5. Gidan rediyon CRI ya bada gagarumar gudumuwa ga masu sauraronsa wajen samar da ilimi ta fannin shirya gasar kacici kacici domin sanin al'adun kasar Sin da tarihi da aikin gona da kuma uwauba yawo shakatawa domin sanin wuraren tarihi na dogon lokaci ga masu sauraro.

6. CRI yana samar da tsaraba ga dukkanin wadanda suka sami lambobin yabo a kan sakamakon gasar da aka shirya domin masu sauraronsa ciki ma har da kai ziyara a kasar Sin ba tare da biyan ko kwabo ba ga mai sauraron.

7.Gidan rediyon CRI ya gina tashoshin gidagen rediyo da dama a kasashen ketare, ciki ma har da nahiyarmu ta Afrika, inda suka hada da Kenya da janhuriyar Niger.

Daga karshe, gidan rediyon CRI yanada kwararrun ma'aikata a kowane sashe, musammam sashen Hausa, don haka ranar rediyo ta duniya abin alfahari ce a gare mu masu sauraro. Muna jinjina ga dukkanin ma'aikatan gidajen radiyo a ko'ina suke a duniya, musamman ma'aikatan sashen Hausa na CRI baki daya, fatarmu Allah ya maimaita mana ameen.

Daga mai sauraronku a ko da yaushe,

Shugaba,

Bello Abubakar Malam Gero Sokoto,

Nigeria.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China