A jihar Yobe alal misali, wani kamfanin kasar Sin mai suna CCECC na gudanar kyakkyawan aikin shinfida kwantar da gwamnatin taraiyar Nigeria ta ba su kwangilar yi a garin Gashua zuwa karamar hukumar Nguru aikin dake wakana a cikin yanayin aiki mai nagarta da inganci. Har wa yau, shekaru 3 da suka wuce, wani kamfanin kasar Sin mai aikin shinfida kwaltar mota ya yi aikin shinfida kwalta mai kyau daga garin Gashua zuwa karamar hukumar Yusufari, lamarin daya samu babban yabo ga kamfanin da ma kasar Sin kana al'ummar karamar hukumar Yusufari dake jihar Yobe sun samu saukin yin tafiye-tafiye. A shekarar 2016, a lokacin da kasashen Nigeria da China suka gudanar da bukukuwan murnar cikon shekaru 45 da kafuwar huldar jakadanci da diplomasiyya, shugaban taraiyar Nigeria ya kai ziyarar sada zumunci a birnin Beijing na kasar Sin inda shugaba Buhari ya yi shawarwari da mahukuntan kasar Sin kana shugabannin kasashen 2 suka taya juna murna kana suka cimma wasu yarjejeniyoyi da juna da suka shafi harkokin tsaro da kuma tattalin arziki.
Dan haka, ina taya kasashen 2 murnar cikon shekaru 46 da kafuwar huldar diplomasiyya da abokantaka da juna a cikin yanayin martaba tagomashin juna tare da yin aiki tare dan amfanuwar kasashen 2 da al'ummominsu.
Daga Alhaji Ali kiraji Gashua, jihar Yobe, tarayyar Najeriya.