in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin Arzikin kasar Sin ya samu tagomashi mai ban mamaki a shekarar 2016
2017-01-23 09:04:59 cri
Zuwa ga sashen Hausa na CRI.

Tare da fatan baki dayan ma'aikatan sashen Hausa suna cikin koshin lafiya a birnin Beijing kamar yadda nake lafiya.

Bayan da shekarar 2016 ta kare sabuwar shekara ta 2017 ta sako kai, matsalar koma bayan tattalin arziki da tasirinta na ci gaba da daukan hankalin duniya sakamakon yadda kawo yanzu kasashe dama ciki har da masu karfin masana'antu suka fada cikin yanayin laluben gano bakin zaren warware matsalar tattalin arzikin da ta dabaibaye su. Tuni dai lamarin ya yi kamari a wasu kasashen inda kasuwar kayayyakin da masana'antu ke samarwa ta ja da baya, farashin danyan mai na ci gaba da shan kayi, ga hauhawar farashin kaya, da dai sauransu.

Sai dai a daidai wannan lokaci da tattalin arzikin kasashe da dama ke cikin halin rashin tabbas, za a iya cewa, lamarin ya sha bamban ga kasar Sin wacce tattalin arzikin ta ke ci gaba da haskaka wa, har ma tana iya taimaka wa sauran kasashen duniya musamman na nahiyar Afirka. Kamar yadda alkaluman da hukumar ba da lamuni ta duniya (IMF) ta fitar suka kara tabbatarwa cewa, kasar Sin ta ba da gudunmawa wajen bunkasar tattalin arzikin duniya da kashi 30% cikin dari. Wannan ba ma kawai ya nuna irin karfin da tattalin arzikin kasar Sin ke da shi ba, har ma ya dada bayyana tasirin sa ga daukacin kasashen duniya.

Ban da wannan, wasu alkaluma da kasar Sin ta fitar a wannan wata na Janairu sun nuna cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya samu koma bayan da bai taba gani ba cikin shekaru 26, bayan da saurin bunkasar tattalin arzikinta ya kai matsayin kashi 6.7 cikin dari. Sai dai duk da haka, wannan matsayin bunkasar tattalin arziki na kasar Sin ya zarce na sauran kasashen da duniya.

Wani abu da ya kara burge ni da tagomashin tattalin arzikin shi ne, yadda wani rahoto ya nuna cewa, kudaden musayan da kasar Sin ta samu sun zarce dalar Amurka tiriliyan 11.

Dangane da haka, ya zama wajibi a yaba wa JKS wacce bisa doronta ne kasar Sin ta samu wadannan manyan nasarori bayan da jagororin jam'iyyar suka fasalta tsarin tattalin arzikin mai siga ta musamman da ya dace da kasar Sin . A halin yanzu, kasar Sin ta riga ta yi wa takwarorinta zarra ta fannin kimiyya, fusaha, noma, tattalin arzikin, da sauransu. Dadin dadawa, kasar Sin ta tasamma 'yanta daukacin al'ummarta daga kangin talauci. Madallah da aiki irin na jagororin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin.

Mai sauraron ku a kullum

Nuraddeen Ibrahim Adam

Shugaban kungiyar

Great Wall CRI Listeners' Club

Kanon Dabo, Nigeria

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China