in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cin karin kumallo yadda ya kamata yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari
2017-01-09 08:49:57 cri

Masana ilmin gina jiki su kan jaddada muhimmancin karin kumallo, kasancewarsa abincin da ya fi kowanne muhimmanci a rana. A Kwanakin baya, wani nazari da aka gudanar a kasar Singapore ya kara jadadda wannan batu, inda Cibiyar nazarin harkokin gina jiki ta Singapore ta ce, karin kumallo yana da matukar muhimmanci ta fuskar sauyawar yawan sukarin da ke cikin jini, don haka cin karin kumallo yadda ya kamata yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari.

Cibiyar nazarin harkokin gina jikin ta kuma tabbatar da cewa, yayin da mutane suka ci karin kumallo da kayan zaki bayan tsakar rana, sun ci abubuwa marasa ma'aunin GI, to, yawan sukarin da ke cikin jininsu a duk rana ya kan yi kasa da sauran mutane sosai.

A kan yi amfani da ma'aunin GI, wato Glycemic Index a Turance, wajen auna adadin sukarin da ke cikin jinin mutum bayan cin wani nau'in abu. Abubuwa marasa ma'aunin GI, kamar hatsin da ba a sarrafa sosai ba, su ne abubuwan da mutane su kan dauki dogon lokaci suna narke su, su kan kosar da mutane na tsahon lokaci, kana yawan sukarin da ke cikin jinin mutane ya kan dauki dogon lokaci yana karuwa, lamarin da ya ba da taimako wajen tabbatar da yawan sukarin da ke cikin jini. A bangare na daban kuma, aikin abubuwa masu yawan ma'aunin GI kamar hatsin da aka sarrafa sosai ya sabawa wancan.

Cibiyar nazarin harkokin gina jiki ta Singapore ta gudanar da nazarin kan maza 11 masu aikin sa kai, inda aka ba su abubuwa iri daban daban a matsayin karin kumallo da kayan zaki bayan tsakar rana, wadannan masu aikin sa kai sun ci abincin rana iri daya, sun ci abincin dare bisa son ransu. Nazarin ya dauki kwanaki 2, inda aka rubuta sauyawar yawan sukarin da ke cikin jininsu. Bayan mako guda kuma, masu aikin sa kan sun yi musayar karin kumallonsu da juna, sun maimaita abun da suka yi a makon da ya gabata.

Masu nazarin sun gano cewa, idan masu aikin sa kan sun ci abincin rana iri daya, sun ci abincin dare bisa son kansu, karin kumallon da suka ci yana matukar muhimmanci a fannin sauyawar yawan sukarin da ke cikin jininsu. Idan sun ci hatsin da ba a sarrafa sosai ba, da dai sauransu, to, a duk rana yawan sukarin da ke cikin jininsu zai yi kasa da wadanda suka ci hatsin da aka sarrafa sosai, kuma haka adadin zai kasance a kashegari.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, kila dalilin da ya sa haka shi ne, wadanda suka ci hatsin da ba a sarrafa sosai ba, suna koshi, don haka ba su ci da yawa, yayin da suka ci abincin rana.

Mai yiwuwa ne yawan sukarin da ke cikin jini fiye da kima, zai kara barazanar kamuwa da ciwon sukari. Don haka masu nazarin sun bada shawarar cewa, kila cin hatsin da ba a sarrafa sosai ba a lokacin karin kumallo yana taimakawa wajen rage barazanar kamuwa da ciwon sukari. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China