in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kuraje suna kara barazanar kamuwa da shan inna da ciwon zuciya
2017-01-01 15:10:23 cri

Wani sabon nazari da aka gudanar a kasar Birtaniya ya gano cewa, masu fama da kuraje sun fi fuskantar barazanar kamuwa da shan inna da ciwon zuciya, saboda haka kamata ya yi masu fama da wannan matsala, su rika gudanar da binciken lafiyarsu lokaci-lokaci, a kokarin gudun kamuwa da cututtukan.

Karambau, wasu kuraje ne masu zafi da ke shafar fuskar dan Adam. Irin wadannan kuraje da wasu kwayoyin cuta ke haddasa su, suna buya ne cikin dogon lokaci a cikin saiwoyin jijiyar dan Adam, a yawancin lokaci, ba sa haddasa kuraje, kuma mutane ba su san sun kamu da kwayoyin cutar ba, amma idan mutum ya fara sun ji gajiya fiye da kima, karfin garkuwar jikinsu ta yaki ciwo ya raunana, ko kuma sun kamu da mura, to, kwayoyin cutar za su haddasa musu kuraje nan take.

Masu nazari daga kwalejin jami'ar London ta kasar Birtaniya sun wallafa rahoton nazarinsu a cikin "mujallar lafiya" cewa, sun tantance bayanan tarihin mutane kusan dubu 320 da ke jinya, wasu dubu 106 daga cikinsu sun taba kamuwa dairin wadannan kuraje. Sakamakon nazarin ya nuna cewa, wadanda suka taba kamuwa da kuraje su da shekaru fiye da 18 amma ba su kai shekaru 40 a duniya ba sun fi masu koshin lafiya fuskantar barazanar kamuwa da shan inna, adadin da ya kai kashi 74 cikin dari, kana kuma barazanar kamuwa da ciwon zuciya da suke fuskanta ya kai kashi 50 cikin dari, in an kwatanta su da masu koshin lafiya.

Amma duk da haka, yiwuwarsu ta kamuwa da shan inna ba ta da yawa sam, saboda haka sakamakon nazarin bai nuna cewa, watakila wadanda suka taba kamuwa da kuraje za su kamu da shan inna ba.

Masu nazarin na kasar Birtaniya sun yi karin bayani da cewa, har yanzu ba a san yadda kurajen suka kara barazanar kamuwa da shan inna da ciwon zuciya ba, amma kamata ya yi masu fama da kuraje su yi taka tsan-tsan game da irin wannan barazana, a saboda haka, kamaya ya yi a rike duba lafiyarsu lokaci-lokaci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China