in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Muhimmacin bakin cakulan wajen yin rigakafin kamuwa da ciwon zuciya da na magudanar jini
2016-12-11 12:11:58 cri

Yanzu haka, bakin cakulan yana kara samun karbuwa a tsakanin mutane a duk fadin duniya sakamakon rashin yawan sukari da mai da kuma amfaninsa ga lafiyar jikin dan Adam. Wani sabon rahoton nazari da aka kaddamar a kasar Switzerland ya yi nuni da cewa, cin bakin cakulan yana taimakawa wajen sassauta matsin lambar da dan Adam ya ke fuskanta, ta yadda cin sa zai iya rigakafin kamuwa da cututtukan da suka shafi zuciya da na magudanar jini.

Masu nazari daga jami'oin Berne da Zurich na kasar Switzerland wadanda su ka wallafa rahoton nazarinsu a cikin "mujallar hukumar nazarin ciwon zuciya ta kasar Amurka" sun nuna cewa, sun zabi rukuni biyu na maza masu koshin lafiya, inda suka bukaci rukunin farko na mazajen da su ci bakin cakulan mai girman 50 na koko a cikinsa, yayin da rukuni na biyu na mazajen suka ci farin cakulan mai giram 50 amma wadanda ba koko a cikinsa ko kuma koko kadan.

Masu nazarin sun gano cewa, idan aka kwatanta su da rukunin farko da rukuni na biyu na wadanda suka ci farin cakulan mai giram 50 wanda babu koko a cikinsa ko kuma kadan, to, a cikin jikin wadanda suka ci bakin cakulan mai girman 50 na koko, yawan wasu sinadaran Hormone da ke jikinsu sakamakon fuskantar matsin lamba ya ragu sosai. Ban da haka kuma, sa'o'i 2 bayan da suka ci bakin cakulan, rashi jin dadi a sakamakon babban matsin lamba da suka fuskanta a jikinsu ya ragu kwarai da gaske.

Masu nazarin na kasar Switzerland sun yi bayani cewa, yawan tunanin da dan Adam ke yi, shi ne musabbin abin da ke haifar da cututtukan zuciya da na magudanar jini. Mai yiwuwa sabon nazarin nasu zai fito da sabuwar hanyar rigakafin kamuwa da irin wadannan cututtuka, amma duk da haka, akwai bukatar ci gaba da nazari don gano yadda bakin cakulan suka taka rawa wajen yin rigakafin kamuwa da cututtukan zuciya da na magudanar jini. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China