in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bincike kan yawan sinadaran Zinc da ke cikin jini yana iya tabbatar da kamuwa da ciwon sankara a mama dake a matsayin farko
2016-10-10 15:03:01 cri

Masu nazari daga kasar Birtaniya sun kaddamar da wani rahoton bincike a kwanan baya wanda ya nuna cewa, bayan sun yi bincike kan yawan sinadaran Zinc da ke cikin jini, sun gano cewa sauyawar yawan sinadarin Zinc da ke jikin dan Adam, yana iya tabbatar da kamuwa da ciwon sankarar mama dake a matsayin farko.

Ana sa ran cewa, masu ilmin kimiyya za su yi amfani da sakamakon wannan nazari, wajen lalubo bakin zaren hanyar tabbatar da kamuwa da ciwon sankarar mama ta hanyar binciken jini cikin sauki.

A shekarun baya, nazarce-nazarce sun nuna cewa, yawan sinadarin Zinc da ke cikin gutsuren sassan maman da ciwon sankara ya kama ya kan karu, amma masu ilmin kimiyya ba su san dalilin da ya sa hakan ba, kana kuma ba sa iya gudanar da bincike mai alaka da hakan a jini ba tare da yin tiyata a jikin dan Adam ba.

Masu nazari daga jami'ar Oxford ta kasar Birtaniya, da kwalejin ilmin kimiyya da fasaha ta kasar sun yi nuni da cewa, sun yi amfani da fasahar tantance sinadaran karfe masu halayya iri daya, wajen gudanar da bincike kan jinin masu fama da ciwon sankarar mama 5, da masu koshin lafiya 5. A baya a kan yi amfani da irin wannan fasaha wajen nazari kan sauyin yanayi da bullar taurari. Masu nazarin sun kuma tantance gutsuren sassan mamar da ciwon sankara ya kama.

Sakamakon nazarin ya nuna cewa, binciken sauyawar yawan sinadarin Zinc da ke cikin jinin dan Adam bisa irin wannan fasaha, zai iya tabbatar da kamuwa da ciwon sankara a mama wanda ke matsayi na farko. To ko mene ne dalilin da ya sa hakan? Dalilin dai shi ne furotin mai kushe da sinadarin Sulfur da ke cikin gutsuren sassan maman da ciwon sankara ya kama, yana raunana kwarewar jikin dan Adam a fannin sarrafa sinadarin Zinc.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, yin amfani da irin wannan fasaha wajen binciken yawan sinadaran karfe da ke jinin dan Adam, ya fi fasahar da ake amfani da ita a halin yanzu inganci, don haka aka fi saurin gano sauyawar yawan sinadaran.

Sakamakon nazarin yana iya taimakawa, wajen lalubo bakin zaren hanyar tabbatar da kamuwa da ciwon sankarar mama, wanda ke a matsayi na farko, ba tare da yin tiyata a jikin dan Adam ba. Har illa yau kuma, an samu sabuwar hanyar yin nazari kan kwayoyin halittun ciwon na sankara.

Baya ga ciwon sankarar mama, nan gaba kuma masu nazarin za su ci gaba da nazarinsu, kan sauyawar yawan sinadaran karfe da ke gutsuren sassan jikin dan Adam da ciwon sankara ya kama. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China