in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shan kofi kafin yin barci a duhun dare kan dakatar da agogon kwakwalwar bil Adama
2016-07-21 17:20:19 cri

Dole ne masu sha'awar shan kofi su lura da cewa, shan tataccen kofi har kwafuna biyu awoyi uku kafin yin barci a duhun dare, ya kan dakatar da agogon kwakwalwar bil Adama da misalin awa daya, lamarin da ke nuna cewa, hakika, bai dace ba a sha kofi kafin yin barci a duhun dare, in ba haka ba, ba za a iya tashi daga barci da sanyin safiya ba, sakamakon rashin yin barci yadda ya kama da dare.

Masu nazari daga jami'ar Colorado ta kasar Amurka sun tattara maza biyu da mata 3, don gudanar da nazari kan su. A cikin kwanaki 49 a jere da suka shafe suna gudanar da nazarin nasu, awoyi 3 kafin wadannan mutane 5 su yi barci a dare, sun sha wata kwayar maganin Caffeine, ko wani sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki, wanda masu nazarin kan bai wa mutanen lokacin da ake gwajin wani sabon magani, ko gudanar da nazari. Yawan sinadarin Caffeine da ke cikin wannan kwayar maganin Caffeine, ya yi daidai da wanda ke cikin tataccen kofi kimanin kwafuna biyu.

Masu nazarin sun tantance yawan sinadarin Melatonin da ke cikin yawun wadannan mutane 5 akai akai. Sinadarin Melatonin yana taka rawa wajen daidaita agogon kwakwalwar bil Adama yadda ya kamata. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, in an kwatanta wadanda suka sha sinadarin da ba shi da wani tasiri ga lafiyar jiki, wanda masu nazarin kan bai wa mutanen lokacin da ake gwajin wani sabon magani ko gudanar da nazari, ya kan dakatar da agogon kwakwalwar wadanda suka sha kwayar maganin Caffeine da mintoci 40 a cikin wani daki maras yawan hasken fitila, sa'an nan idan a cikin wani daki mai yawan hasken fitila suke tsawon awoyi uku, to a kan dakatar da agogon kwakwalwarsu da mintoci 85. Har wa yau, idan a cikin irin wannan daki mutum yake kuma ya sha wata kwayar maganin Caffeine, to, hakan na dakatar da agogon kwakwalwarsa da mintoci 105 baki daya.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon nazarinsu ya kara shaida cewa, bai dace a sha kofi kafin a yi barci a duhun dare ba! Amma masu yawon shakatawa suna iya cin gajiyar shan kofi kafin su yi barci a duhun dare. Shan kofi a lokacin da ya dace, yana iya taimaka musu wajen warware matsalar bambanci lokaci, yayin da suke yawon shakatawa a sassa daban daban na duniya.

Bayan haka kuma, sakamakon wannan nazari yana da muhimmiyar ma'ana wajen jinyar masu fama da wata matsala ta sauyin yanayin jikinsu a tsawon sa'oi 24 (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China