in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Asibitocin Amurka da dama sun karfafawa iyaye mata gwiwar shayar da jariransu nonon uwa zalla
2016-05-16 07:40:37 cri

Cibiyar shawo kai da yin rigakafin cutattuka ta kasar Amurka wato CDC ta kaddamar da wani rahoton bincike a kwanan baya, inda ta bayyana cewar, karin asibitocin kasar suna karfafa gwiwar iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba, su shayar da jariran nasu nonon uwa zalla, matakin da cibiyar ta jaddada cewa, yana taimakawa lafiyar jarirai sabbin haihuwa da iyayensu mata sosai. Rahoton ya nuna cewa, daga shekarar 2007 zuwa shekarar 2013, yawan asibitocin kasar da suke aiwatar da matakai guda 10 da MDD ta gabatar dangane da kara jaddada muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa zalla, ya ninka kusan sau daya, wato adadin ya kai kashi 54 cikin dari bisa jimillar asibitocin kasar. Kana kuma yawan asibitocin kasar da suka taimakawa iyaye mata su shayar da jariransu nonon uwa zalla cikin awa daya bayan haihuwa ya karu zuwa kashi 65 cikin dari bisa jimillar asibitocin kasar. Ban da wannan kuma, yawan asibitocin kasar da suka ilmantar da masu juna biyu kan muhimmancin shayar da jariransu nonon uwa zalla da kuma ba da jagora ga iyaye mata da suka haihu ba da dadewa ba kan shayar da jariransu nonon uwa zalla, ya kai kashi 90 cikin dari. Cibiyar CDC ta yi bayani da cewa, shayar da jarirai nonon uwa zalla yana da amfani sosai a wasu fannoni, alal misali, rage barazanar da jarirai ke fuskanta wajen kamuwa da cututtuka a kunne, hanyoyin numfashi, tumbi da hanji, da kuma ciwon asma, matsalar kiba, da mutuwar jarirai ba zato ba tsammani da dai sauransu. Har wa yau shayar da jarirai nonon uwa zalla yana taimakawa iyaye mata su rage barazanar kamuwa da ciwon sukari, ciwon zuciya, da ciwon sankarar mama, da kwan mace. A takaice dai, ana ganin cewa, shayar da jarirai nonon uwa zalla zai rage wa gwamnatin Amurka a kalla dalar Amurka biliyan 2 ko fiye da haka da ta ke kashewa wajen jinyar kananan yara a ko wace shekara. Yanzu haka an shayar da jarirai sabbin haihuwa da yawansu ya kai misalin kashi 80 cikin dari nonon uwa zalla. Amma daga cikinsu, ana shayar da rabin wannan adadi kawai nonon uwa zalla ne bayan watanni fiye da 6 da haihuwarsu. Matakai guda 10 da MDD ta gabatar dangane da kara azama kan shayar da jarirai nonon uwa zalla sun hada da fara shayar da jarirai nonon uwa zalla cikin awa daya bayan haihuwarsu, sanya jarirai sabbin haihuwa da iyayensu mata su zauna cikin daki guda yayin da suke asibiti, kada a shayar da jarirai sabbin haihuwa wasu nau'o'in abinci da abin sha baya ga nonon uwa, idan ba likitoci ba ne suka bayar da umarnin yin haka. (Tasallah Yuan)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China