in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Idan iyayen yaro suna tafiya yayin barci, yaron kan iya gadon wannan halayya
2016-04-02 17:00:54 cri

Sakamakon wani sabon nazari da aka yi a kasar Canada, ya shaida mana cewa, yin tafiya yayin barci na da nasaba da gadon dabi'un halitta. Idan iyayen wani yaro sun taba yin tafiya yayin barci, to, yaron su na iya fuskantar yiwuwar gadon wannan dabi'a da kaso sama da kashi 60 cikin dari.

Nazarin ya yi nuni da cewa, kwayoyin dabi'ar halitta da mu 'yan Adam muke da su, suna da babban tasiri kan yiwuwar kamuwa da matsalar yin tafiya yayin barci. Wato idan a baya iyayen wani yaro sun taba fama da matsalar yin tafiya yayin barci, musamman ma idan dukkansu sun taba fama da matsalar, to, ana iya hasashen cewa, dan su zai yi tafiya yayin barci, saboda haka, kamata ya yi a share fage sosai.

Ma'anar yin tafiya yayin barci ita ce, yin tafiya ko yin wani abu yayin da wani ke yin barci, kuma ko da yake ya tashi amma bai farka ba, kana kuma idan ma ya farka ba zai tuna ba. Wannan wata matsala ce da kananan yara kan yi fama da ita, bayan sun shiga lokacin balaga, matsalar kan bace sannu a hankali. Masu nazari daga asibitin Sacred Heart na Montreal na kasar Canada, sun tantance bayanan barci da suka shafi kananan yara kusan dubu 2, da aka haife su daga shekarar 1997 zuwa shekarar 1998 a lardin Québec na kasar Canada, tare da binciken tarihin iyayensu na yin tafiya yayin barci, a kokarin kara sanin wanna matsalar da kananan yara ke fuskanta.

Masu nazarin sun gano cewa, wasu da yawansu ya kai kaso 29.1 cikin dari daga cikin wadannan kananan yara, sun taba yin tafiya yayin barci kafin shekarunsu na haifuwa su kai 13 a duniya, musamman ma idan suna da shekaru 10 a duniya. A cikin yaran da iyayensu ba su taba yin tafiya yayin barci ba, wasu yaran da yawansu ya kai kashi 22.5 cikin dari ne kawai suka taba yin tafiya yayin barci, amma idan mahaifi ko mahaifiya ta taba yin tafiya yayin barci, to, irin wannan adadi ya kai 47.4 cikin dari. Idan dukkan iyayen yaran sun taba yin tafiya yayin barci, adadin yana kaiwa kashi 61.5 cikin dari.

Yin ihu yayin barci, wata matsala ce ta daban, wadda kananan yara kan yi fama da ita. An gano cewa, rabin kananan yara sun taba yin ihu ba zato ba tsammani yayin da suke barci. Idan wani yaro ya taba yin ihu yayin barci kafin shekarunsa sun kai 4 da haihuwa, to, ya kan fuskanci babbar yiwuwar yin tafiya yayin barci kafin shekarunsa sun kai 13 da haihuwa. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China