in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kada a yanke wa kananan yara hukuncin kamuwa da ciwon gazawa wajen iya karanta haruffa daidai ko dyslexia a turance
2016-04-05 10:06:23 cri

Kwanan baya, jami'ar Newcastle ta kasar Birtaniya, ta kaddamar da wani sakamakon nazari, inda a cewarta, idan aka gaggauta yanke wa kananan yara hukuncin kamuwa da ciwon gazawa wajen iya karanta rubutu na haruffa daidai ko dyslexia a turance, mai yiwuwa ne hakan ya haifar da illa ga yadda malamai suke koyar da yaran. Matakin da kuma ka iya sa wadannan kananan yara su rasa damar maido da kwarewarsu ta karantu da rubutun haruffa daidai.

Masu nazari daga jami'ar Newcastle sun gayyaci malamai 267 daga makarantun firamare guda 23 da ke kasar Birtaniya, domin shiga gwaje-gwaje, tare da amsa tambayoyi a rubuce. Masu nazarin sun tantance ra'ayoyinsu game da ciwon dyslexia, da 'yan makarantar firamare suka kamu da shi, da kuma matsalar karanta haruffa da suke fama da ita.

Sakamakon gwaje-gwajen ya nuna cewa, yawancin malaman suna ganin cewa, bai wa 'yan makarantar firamare wadanda suke fama da matsalar karanta haruffa taimako cikin himma da kwazo kuma cikin dogon lokaci, kan haifar da sakamako mai kyau. Amma yawancinsu na ganin ba da karfin zuciya sosai kan kananan yaran da suka kamu da ciwon dyslexia, ba zai sauya halin da suke ciki ba.

Ciwon dyslexia, wani nau'in ciwo ne da ke haifar da matsaloli ga kananan yara wajen yin karatu yadda ya kamata. Wadanda suke fama da ciwon, su kan yi fama da matsalar karanta haruffa, ta hanyar kasa banbance haruffa masu kama ta fuskar sautin furta su. Kaza lika wannan ba ya nuna cewa yaran dake fama da wannan matsala suna da karancin basira, duk da cewa akwai babban bambanci a tsakaninsu da mu masu koshin lafiya a kwakwalwarsu a fannonin fahimtar haruffa, da karanta su, da rubuta kalmomi da rubuta bayanai.

Duk da haka abu ne mai wahala a iya bambance kananan yaran da suka kamu da ciwon dyslexia, da kuma wadanda suke fama da matsalar karanta haruffa. Ana bukatar dogon lokaci na koyarwa, da duddubawa wajen gano ainihin matsalolin da wani yaro ke fuskanta a fannin karatu.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, sakamakon nazarinsu ya shaida cewa, yanke wa wani yaro hukuncin kamuwa da ciwon dyslexia cikin sauri, kan haifar da illa ga yadda malamansu suke koyar musu. Saboda haka malamai da yawa suna ganin cewa, da wuya a iya warkar da ciwon dyslexia ta hanyar koyar da mai fama da shi cikin himma da kwazo, lamarin da ya sa wata kila wasu daga kananan yaran da suke fama da matsalar karanta haruffa, su rasa damar maido da kwarewarsu ta yin karatu sakamakon taimakon malamansu. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China