Assalamu Alaikum sashen hausa na gidan rediyon kasar sin cri hausa, a hakikanin gaskiya mu al'ummar najeriya munga amfanin dangantakar kasar sin da kasarmu najeriya duba da yadda muke samun ingantattun kaya masu rahusa wanda yanzu haka dik gidan kabi zaka ga ana amfani da kayan kasar sin, gaskiya munyi na'am da dangantakar wannan kasa da kasarmu najeriya, abin burgewa da kuma ban shawa sai kasar sin ta buda wannan tasha mai albarka wacce zata bamu damar sanin abinda ke faruwa a kasashen duniya gakuma shirye shirye masu kayatarwa dakuma karin haske kan al'adun sinawa, lallai idan babu wannan tasha bansan hanyar da yan najeriya zasu bi ba domin sanin al'adun sinawa, wannan tasha ta samu karbuwa daga kasashe daban daban na duniya ciki kuma harda najeriya, wanda yanzu haka har yasa wasu yan najeriya sanin al'adun sinawa kamar suma yan kasar sin ne, ina fatan Allah yasa dangantaka tsakanin kasar sin da najeriya ta zama mai alheri.
Daga Abdullai Muhammad Maiyama