in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rashin isasshen barci ga kananan yara yana iya sanya su kara yin ciye-ciye
2016-03-21 07:25:34 cri

Wani sabin nazari da aka gudanar a baya-bayan nan ya shaida cewa, wasu kananan yara wadanda ba su samu isasshen barci ba su kan yi kiba nan da nan, duk da haka babu wani bincike da ya bayyana yadda barci yake haifar da illa ga yawan abubuwan da kananan yara suka ci.

Kwanan baya wani sabon nazari da wasu masana daga kasasr Ingila suka yi ya nuna cewa, idan kananan yara wadanda shekarunsu ba su wuce 6 a duniya ba suka yi barcin kasa da sa'o'i 11 a ko wace rana, to, za su bukaci kara cin abubuwa, musamman ma kayan kwalama, wadanda ke sanya mutum kiba cikin sauki.

Masana suna ganin cewa, kamata ya yi kananan yara wadanda shekarunsu ba su wuce 6 a duniya ba su rika yin barcin sa'o'i 11 zuwa 12 a ko wace rana. Binciken da aka yi a kan baligai ya nuna cewa, rashin isasshen barci ya kan sanya kwakwalwa ta rika aikewa da sakon kara cin abubuwa ga mutane domin biyan bashin barci da ba a yi a baya ba.

Masu nazari daga jami'ar London ta kasar Ingila sun wallafa rahotonsu a mujallar nan da ke sharhi kan "matsalar cutar kiba ta kasa da kasa", inda a cewarsu, sun gudanar da nazarinsu ne kan kananan yara dubu 1 da 8 wadanda shekarunsu suka kai 5 da haihuwa, kuma suna shafe matsakaicin lokacin da ya kai sa'o'i 11 da rabi a ko wace rana suna barci. Sakamakon nazarin ya shaida cewa, idan an kwatanta kananan yaran da ke barcin da bai wuce sa'o'i 11 ba, da kuma wadanda suke shafe sa'o'I 11 suna barci, kananan yaran da ba su samu isasshen barci ba sun fi son cin abubuwan masu dandano, don haka su ke yin kiba nan da nan.

Sabili da haka, masu nazarin sun ba da shawarar cewa, idan har ana son hana kananan yara su yi kiba, kamata ya yi a hana wadanda ba su samu isasshen barci ba yawan kallon abubuwan masu zaki. Ko shakka babu abu mafi muhimmanci shi ne iyaye su tabbatar da cewa, 'ya'yansu sun samu isasshen barci.

Haka zalika masu nazarin sun yi nuni da cewa, ko da baligai ko kuma kananan yara, rashin isasshen barci kan sanya 'dan Adam kara cin abubuwa kamar mayar da martani. Yanzu haka ana iya samun kayayyakin kwalama a ko ina ba tare da wata matsala ba, don haka kamata ya yi a yi taka tsan-tsan wajen cin irin wadannan kayayyakin makulashe a kokarin mai da miyun bayan da aka yi fama da rashin isasshen barci.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China