in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hakoran kananan yara kan rube cikin sauri sakamakon shan taba a gidan su
2016-03-14 09:21:54 cri

Idan ana shan taba a gidan da wani karamin yaro ke rayuwa, to, watakila hakan ya sanya hakoran wannan yaro su rube!

Masu nazari a kasar Japan, sun kaddamar da rahotonsu a kwanan baya, cikin "mujallar ilmin likitanci ta kasar Ingila", wanda ya nuna cewa idan ana shan taba a gidan dake da karamin yaro, hakn na haifar masa da barazanar rubewar hakora, kafin ya kai shekaru 3 a duniya. Rahoton ya nuna cewa wannan barazana na karuwa da ninka biyu, idan aka kwatanta da ta karamin yaron da babu mai shan taba a gidan su.

Masu nazarin daga jami'ar Kyoto ta kasar Japan sun tantance adadin da ya shafi kananan yara fiye da dubu 70, wadanda aka haife su tsakanin shekarar 2004 zuwa 2010, inda akwai masu shan taba a gidajen kashi 55.3 cikin dari daga cikinsu. Barazanar rubewar hakora ga wadannan kananan yara suke fuskanta, ta ninka kusan sau daya da rabi sama da na sauran.

Har wa yau, idan mambobin iyalin wani karamin yaro suna shan taba a gabansa, to, barazanar rubewar hakoran sa da yake fuskanta ta ninka sau 2 ko fiye da haka sama da ta sauran.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, sakamakon shakar hayakin tabar da aka sha, ya kan sa abubuwan da ke cikin yawun mutane su sauya, wanda hakan ke sanyawa kwayoyin cutar da suke sa hakora su rube su taru a baki, ta yadda hakora kan rube, tare da kasancewar abubuwa marasa tsabta a kan hakoran.

Sabili da haka ne ya kamata baligai, su mai da hankali kan yadda suke rayuwa ta hanyar da ta dace, a kokarin ganin kananan yara sun girma yadda ya kamata.

Har ila yau, wasu masu nazari daga kasar Jamus sun dauki tsawon lokaci suna gudanar da wani nazari, inda suka gano cewa, hakoran masu shan taba kan fadi kafin na marasa shan taba, amma idan sun daina shan taba, barazanar faduwar hakoran na su za ta dan ragu.

Masu nazarin sun yi nuni da cewa, mai yiwuwa ne shan taba ya haifar da gyambon dasashi, ta yadda hakoran kan fadi kafin lokaci. Idan kuma mutum ya daina shan taba, barazanar faduwar hakoransa za ta ragu. Duk da haka, idan yana son ci gaba da rage wannan barazana, ya zama dole ya daina shan taba har shekaru 10 ko fiye da haka.

Baya ga ba da kariya ga hakora, daina shan taba yana iya tabbatar da lafiyar jijiya, da zuciya, da huhu. A karshe kuma hakan yana iya tsawaita rayuwar mutane. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China