in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dalilin da ya sa jikin yaran da ke zama a yankunan karkara ke iya karbar bakin abubuwa
2016-03-05 14:39:16 cri

Sanin kowa ne cewa, ba kamar yaran da ke rayuwa a birni ba, galibin takwarorinsu da ke zama a yankunan karkara ba safai jikinsu ya kan ki wasu bakin abubuwa ba, kana da wuya su kamu da cutar matsalar nunfashi ko asma.

Kwanan baya, masu nazari daga daga jami'ar Ghent ta kasar Belgium sun gabatar da wani sabon dalilin da ke haddasa hakan, a cewarsu, mai yiwuwa ne wani irin nau'in sinadarin furotin na A20 da ke jikin kananan yara mazauna yankunan karkara suna iya taimaka wa huhun yaran karbar wasu bakin abubuwa.

Masu nazarin sun wallafa rahotonsu cikin sabuwar mujallar "Kimiyya" ta kasar Amurka, inda suka yi bayani cewa, a cikin gwaje-gwajen da suka gudanar, sun bar beraye su taba kasar da aka debo daga gonakin kasashen Jamus da Sweden. Bayan tsawon lokaci, jikin wadannan beraye sun fara karbar wani nau'in karamin kwaro mai kama da kudin cizo, wanda ke da illa ga jikin mutane a duk fadin duniya.

Masu nazarin sun ci gaba da nazarinsu, inda suka gano cewa, kasar da Berayen suka taba ya sanya nau'in sinadarin furotin na A20 ya bullo a jikin berayen, ta yadda zai iya taimakawa sassan jikin berayen da ke amfani da su wajen yin numfashi karbar wasu abubuwa. Idan wannan sinadarin furotin bai yi aiki yadda ya kamata ba, to, taba kasar da aka debo daga gonakin ba zai iya ci gaba da kare berayen daga fama da cutar matsalar nunfashi wato asma ko kuma taimaka musu karbar wasu bakin abubuwa ba.

Ban da haka kuma, masu nazarin sun yi bincike kan kananan yara dubu biyu da suka girma a gonaki. A karshe, sun tabbatar da cewa, hakika, da wuya yawancinsu su kamu da ciwon asma yayin da jikinsu ya karbi wasu bakin abubuwa. Kalilan daga cikin su kuma, nau'in sinadarin kwayar dabi'ar halittarsu ta A20 ta sauya, don haka ba ta iya fitar da nau'in sinadarin furotin na A20 yadda ya kamata.

Masu nazarin sun yi bayani da cewa, nan gaba za su tabbatar da abubuwan da ke cikin kasar da aka debo daga wancan gonaki, inda har aka samu snau'in sinadarin furotin na A20 a ciki. Yanzu suna zaton cewa, watakila wani nau'in kwayar cuta ce da a kan samu a wuraren kiwon shanu ita ce ke fitar da nau'in sinadarin furotin na A20.(Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China