in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ya zama tilas a mai da hankali kan abubuwa masu guba da ke tufafinku!
2016-02-22 09:57:41 cri

A kan yi amfani da sinadarai masu yawa na magunguna yayin da ake saka, da kuma lokacin dab'i da tiri, saboda haka ya zama tilas mu mai da hankali kan tufafin da muke saya.

Masu nazari daga jami'ar Stockholm ta kasar Sweden sun gudanar da wani nazari a kwanan baya, inda suka gano cewa, ana barin abubuwan magunguna da yawa kan tufafinmu na yau da kullum, kuma watakila wasu abubuwan masu guba za su iya kawo illa ga lafiyar mutum ba tare da ya lura ba, musamman wadanda ba a iya gani, ko a iya ji ba.

Masu nazarin sun yi bincike kan tufafi guda 60 da aka saka a kasar Sweden da sauran kasashe. Kwarya-kwaryar sakamakon nazarin ya nuna cewa, wadannan tufafi suna kunshe da dubban nau'o'in sinadarai, wadanda ake iya bambance wasu nau'o'i dari daya daga cikinsu. A cikin wadannan sinadarai, wasu su na samuwa ne yayin da ake saka tufafin, wasu kuma watakila suna hawa yayin da ake jigilar tufafin.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, taba wadannan sinadarai na iya kara mana barazanar kamuwa da gyambon fata sakamakon bijirewar da jikinmu ke yi musu. Haka kuma watakila irin wadannan sinadarai na iya kara kawo illa ga lafiyar dan Adam da muhallin halittu, kuma wasu daga cikinsu ana nuna shakku kan ko su ne abubuwan da suke haddasa ciwon sankara, yayin da wasu suke sa wa halittun da ke rayuwa cikin ruwa guba.

Masu nazarin sun zabi sinadarai masu nau'o'i guda hudu domin kara tantance su, bisa ga ko a kan yi amfani da wadannan sinadarai a kullum ko a'a, ko ana amfani da su da yawa ko a'a, ko akwai guba da yawa cikin wadannan abubuwan magunguna ko a'a, ko suna iya shiga cikin fatar mutum ko a'a.

A karshe dai, masu nazarin sun gano cewa, a cikin tufafin da aka saka da nau'in yadi na leda a maimakon auduga, yawan sinadarin Quinoline da sinadarin Aromatic Amine sun fi yawa. A cikin tufafin da aka kera da auduga kuwa, yawan sinadarin Benzothiazole ya fi yawa, har ma ana rage sinadarin a cikin tufafin da aka saka da auduga, wadda aka shuka ba tare da amfani da sinadarai ba.

Sinadarin Quinoline na da guba, wanda ke sawa mutane su ji kaikayi a fatar su. An kuma hana amfani da sinadarin Aromatic Amine wajen yin rini, saboda yana iya haddasa ciwon sankara. Ban da haka kuma, sinadarin Benzothiazole shi ma yana da guba, yana iya sa idon mutum ruwa, kuma ana jin kaikayinsa a fata, kana kuma sinadarin yana iya gurbata ruwa.

Haka zalika, masu nazarin sun wanke tufafin da suka yi bincike, inda suka gano auna yawan sinadarai da suka rage. Wasu akan wanke su baki daya, amma duk da haka suna ci gaba da gurbata ruwa. Wasu kuma suna ragewa a jikin tufafin. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China