in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mai yiwuwa kwaramniyar zirga-zirgar motoci ka iya rage tsawon ran dan Adam
2016-02-13 13:06:00 cri

Masana na ganin cewa, watakila zama a gidajen da ke kusa da gefen hanyar mota bai dace ba!

Kwalejin nazarin kimiyya da fasaha da ke kasar Ingila ya kaddamar da wani sabon rahoton nazari a kwanan baya, inda ya ke ganin cewa, mai yiwuwa ne yawan kara da kwaramniyar motoci za ta iya rage tsawon ran dan Adam.

Masu nazari daga kwalejin koyon kimiyya da fasaha da ke kasar Ingila, kwalejin ilmin kiwon lafiya da cututtuka a yankuna masu zafi na jami'ar London da sauran hukumomi sun gudanar da wannan nazari, inda suka yi nazari kan yanayin koshin lafiyar mazauna birnin London kimanin miliyan 8 da dubu 600 da kuma matsayin kwaramniyar zirga-zirgar motoci a wurare da dama a London da safe da kuma yamma daga shekarar 2003 zuwa 2010. A cikin wadannan shekaru 8, baligai fiye da dubu 440 daga cikin wadannan mazauna birnin sun mutu sakamakon dalilai daban daban.

Masu nazarin sanya mutanen da shekarunsu suka wuce 25 a duniya a matsayin rukunin baligai, yayin da suka kasafta wadanda shekarunsu suka zarce 75 da haihuwa a matsayin rukunin tsoffafi. Sun gano cewa, yawan baligai da tsoffafi da suka mutu a wuraren da matsayin kwaramniyar zirga-zirgar motoci ya wuce ma'aunin sauti na DB 60 da safe, ya fi na wadanda suke zama a wurare marasa hayaniya da kashi 4 cikin dari.

Masu nazarin sun yi bayanin cewa, yawancin mutanen sun mutu ne sakamakon ciwon zuciya da cututtukan da suka shafi kayan cikin da ke taimakawa gudanar jini, lamarin da watakila sun faru ne sakamakon kwaramniyar da zirga-zirgar motoci take haifar, kamar hawan jini, matsalar isasshen barci, yawan tunani. Ban da haka kuma, yawan baligai da tsoffafin da ke zama a wurare masu kwaramniyar zirga-zirgar motoci da safe da aka kai su asibiti sakamakon kamuwa da cutar shan inna, ya fi wadanda suke zama a wurare marasa hayaniya a kalla da kashi 5 cikin dari.

A cewar masu nazarin, ko da yake ya zuwa yanzu ba a iya tabbatar da cewa,mummunar illar da kwaramniyar zirga-zirgar motoci take haifar wa lafiyar mutum ta fi illar da shan taba, rashin isasshen motsa jiki, yadda a kan ci abinci suke haddasawa ba. Amma sakamakon wannan nazari ya shaida mana cewa, kwaramniyar zirga-zirgar motoci tana yin illa ga lafiyar mutum, don haka ya zama wajibi a ci gaba da nazari a wannan fanni. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China